Ba mu dage takunkumin hana yakin neman zaben 2019 ba- Hukumar INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC ta gargadi ’yan siyasa da jam’iyyu da su nisanci duk wani mataki na yakin naman zabe saboda ya saba wa doka. Humumar zaben ta bayyana cewa tuni ta fara aiki a kan kasafin kudin zabe na shekarar 2019. Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu shi ne ya bayyana haka […]

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta INEC ta gargadi ’yan siyasa da jam’iyyu da su nisanci duk wani mataki na yakin naman zabe saboda ya saba wa doka.
Humumar zaben ta bayyana cewa tuni ta fara aiki a kan kasafin kudin zabe na shekarar 2019.
Shugaban Hukumar Farfesa Mahmood Yakubu shi ne ya bayyana haka yayin wani taron tattaunawa da manema labarai da hukumar ta yi a jiha a Abuja.
“Ina gargadin ’yan takara da jam’iyyu cewa ba mu fitar da jadawalin harkokin zabe ba. Duk wani yakin neman zabe da wani ya yi ya saba wa doka. Ya zama wajibi su dakata har sai mun fitar da jadawalin zabe”. Inji shi.