Ba mu dakatar da ƙudirorin Dokar Haraji ba — Majalisar Dattawa
A wannan Alhamis ɗin ce Majalisar Dattawan Najeriya ta ce har yanzu ba ta janye ƙudirorin Dokar Haraji ba tana mai jaddada aniyar ci gaba da tattaunawa a kansu. Shugaban Masu Rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele — na jam’iyyar APC da ke wakiltar Ekiti ta Tsakiya — ne ya bayyana hakan yayin da yake janyo hankalin […]
A wannan Alhamis ɗin ce Majalisar Dattawan Najeriya ta ce har yanzu ba ta janye ƙudirorin Dokar Haraji ba tana mai jaddada aniyar ci gaba da tattaunawa a kansu.
Shugaban Masu Rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele — na jam’iyyar APC da ke wakiltar Ekiti ta Tsakiya — ne ya bayyana hakan yayin da yake janyo hankalin Majalisar Dattawan kan maganar da ake yaɗawa cewa sun dakatar da tattaunawa game da ƙudurorin.
- Yadda rasuwar fitaccen mawaƙi El-Mu’az ta girgiza Kannywood
- Boko Haram: Fararen hula 10,000 sun mutu a hannun sojojin Najeriya — Amnesty
Dangane da hakan ne Shugaban majtalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya goyin baya yana mai cewa majalisar za ta yi duk mai yiwuwa domin kare muradun ’yan ƙasar ba tare da shakku ba.
“Babu wanda zai tursasa Majalisar Dattawa. Duk wani gyara da muke tunani za a yi amfani ga ’yan ƙasar nan, za mu yi aiki a game da hakan.
“Waɗannan ƙudurorin suna ɗauke da abubuwa masu amfani ga Najeriya,” a cewar Akpabio.
Akpabio ya ce ba gaggawa suke yi ba, don haka ya ce za su yi aiki a tsanake kan ƙudurorin kafin ɗaukar wani mataki.
Ya ce taron masu ruwa da tsaki da za a yi a nan gaba ne zai bayar da dama domin tattaunawa tare da nemo hanyoyin da za a magance duk matsalar da ake fargaba tana tattare da ƙudurorin.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da a jiya Laraba Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Barau Jibrin, ya ce an jingine batun ne saboda yadda ake ce-ce-ku-ce a kan ƙudurorin, da kuma tabbatar da cewa an yi duban tsananki kan ɓangarorin da wasu al’ummar ƙasar ke nuna damuwa a kai.
Ya ƙara da cewa an kafa wani kwamiti na Majalisar Dattawa ƙarƙashin Sanata Abba Moro da zai zauna da ofishin Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’ar Ƙasar don duba ɓangarorin da suke janyo taƙaddama don a warware su tare da dawo mata da su gabanin zaman sauraron ra’ayin jama’a a kansu.
“Mun yanke hukuncin jingine batun siyasa da ɓangaranci da ƙabilanci a gefe, mu zauna mu-ya-mu, don mu lalubo mafita kan batun Ƙudurorin Gyara kan Dokokin Haraji,” a cewar Sanata Barau.
“Mun sanar da ɓangaren zartarwa matsayarmu, kuma an amince cewa za a kafa wani kwamiti da zai zauna ya yi duba kan ɓangororin da ake taƙaddama a kansu don a warware su.”
Ya ce an ɗauki matakin ne “domin ƙasar ta Nijeriya ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.
“Za mu warware dukkan batutuwan kafin a bar komai ya wuce,” in ji Sanata Barau.
Barau ya kuma bayyana sunayen Sanata Titus Zam, Orji Uzor Kalu, Sani Musa da Abdullahi Yahaya a matsayin wasu daga cikin mambobin kwamitin.
Barau, wanda ya jagorancin zaman majalisar, yace kudurorin sun janyo cece kuce, inda yace an dorawa kwamitin alhakin tuntubar Antoni Janar na Tarayya, da ɓangaren zartarwa da sauran muhimman masu ruwa da tsaki.
A ranar 3 ga watan Oktoban daya gabata, shugaba Bola Tinubu, ya aike wa Majalisar Dokokin Najeriya da ƙudirorin haraji guda 4, a cikin wasiƙar da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, suka karanta a zaman zaurukan majalisun daban-daban.