Ba mu fitar da wanda za mu zaba tsakanin Atiku da Buhari ba – Miyetti Allah

A karshen wannan makon ne kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta gudanar da taronta na kasa da ya samu halarcin wakilanta na jihohi. Aminiya ta tattauna da babban Sakataren Kungiyar Injiniya Saleh Alhassan inda ya yi bayani a kan wasu batutuwa ciki har da matsayarsu a kan zaben 2019 da ke tafe: […]

Ba mu fitar da wanda za mu zaba tsakanin Atiku da Buhari ba – Miyetti Allah

Injiniya Saleh Alhassan

A karshen wannan makon ne kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta gudanar da taronta na kasa da ya samu halarcin wakilanta na jihohi. Aminiya ta tattauna da babban Sakataren Kungiyar Injiniya Saleh Alhassan inda ya yi bayani a kan wasu batutuwa ciki har da matsayarsu a kan zaben 2019 da ke tafe:

Ko za a danganta wannan taro naku da siyasa kasancewar ana cikin lokacinta a yanzu?

Duk wani lamari da zai tara jama’a bai rasa nasaba da siyasa a yanzu. Sai dai muhimmin abin da ya taramu a nan shi ne siyasarmu ta cikin gida inda wakilan jama’a a karkashin kungiyarmu da suka taho daga jihohin kasar nan 36 da Abuja suka sake jaddada zabar shugabannin kungiyar a matakin kasa karkashin jagorancin Alhaji Abdullahi Bello Bodejo a wani sabon wa’adi na shekara hudu. Haka mun tattauna a kan bullar wata cuta a Jihar Kogi musamman a yankunan kananan hukumomin Dekena da Ayingba inda zuwa yanzu cutar ta kashe mana jama’a sama da 200. Mun bayyana bukatar daukar matakan gaggawa daga jami’an kiwon lafiya musamman masu yaki da bullar cututtuka su binciki lamarin tare da kai musu dauki don magance yaduwarta. Haka jami’an tsaro su gudanar da bincike a kai kasancewar mu makiyaya muna da makiya ta ko’ina.

Ka yi magana a kan dokar hana kiwo a Jihar Benuwai ko akwai wani sabon abu ne kan lamarin?

Ba za mu gushe muna magana a kan lamarin Benuwai ba har sai an yi mana adalci. Saboda wannan al’amari ya jawo yaduwar rigingimun da jama’armu ke fama da su zuwa wasu jihohi kamar Taraba da Nassarawa da Kogi da kuma Kuros Riba sakamakon kaura da wadansu makiyaya suka yi daga yankunansu na kakanni a jihar zuwa jihohin. Wannan ya jawo karin cunkushewar Fulani masu kiwo a wuraren inda hakan ke haddasa karin rigingimu a kan filaye. Sannan sama da matasanmu 300 daga cikin wadanda suka ci gaba da zama a jihar na tsare a gidajen kurkuku a jihar a yanzu haka dalilin dokar hana kiwo da jihar ta kafa wanda muke shari’a a kai sama da shekara daya. Ga kuma azabtarwa da kisa daga bangaren jami’an tsaron hana kiwo da gwamnatin jihar ta kafa. Sannan dokar da jihar ta kafa shi ne mafi muni a iya saninmu ba wai a nan Najeriya kadai ba har ma da daukacin kasashen Yammacin Afirka baki daya kasancewarsa an tsara shi ne don musgunawa da kuntata wa nau’in wata al’umma daya wato Fulani makiyaya. Sai dai alhamdulillahi bayanan da suke fitowa daga bakin wadansu mashahuran ’yan siyasar jihar na baya-bayan nan shi ne gaskiya ta bayyana. Sanata George Akume ya fada karara cewa akwai hannun gwamnatin jihar a kashe-kashen da ke faruwa inda ake amfani da kungiyar ’yan banga masu sa ido a kan dabbobi da gwamnatin ta kafa.

’Yan takarar Shugaban Kasa na manyan jam’iyyu wato Shugaba Muhammadu Buhari na APC da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar na PDP mambobi marasa rajista na Miyetti Allah ne kasancewarsu Fulani, shin wanne ne a cikinsu za ku mara wa baya?

Mun ji dadi da aka samu hakan ko ba komai ya magance zafin siyasar kabilanci da ta addini da bangaranci da aka fuskanta a zaben baya ba za a samu a yanzu ba. Ko ba komai labaran makiyaya da manoma da ya mamaye kafofin watsa labarai a baya a yanzu ya ja baya. Muna sa rai hakan zai takaita yin kamfe a kan mas’alolin da suka shafi al’umma kawai, wanda dama shi siyasa ta gada. Idan na koma ga tambayarka ba mu da wani dan takara a tsakaninsu da muka fitar zuwa yanzu. Za mu tsaya mu saurari manofofinsu a cikin tsanaki sannan mu ji tanadin da kowannensu ke da shi a kan al’ummanmu mu kasa a faifai. Dole kowannensu ya nuna mana tsare-tsarensa da tanadinsa a kan kiwo, wannan shi ne za mu yi amfani da shi wajen mara wa wanda muka gamsu da shi baya idan lokacin ya yi mu bayyana. Kuma wannan bai takaita a kan jam’iyyun nan biyu kadai ba saboda muna da jam’iyyu sama da 90 a kasar nan da ke da manofofi da tsare tsare iri-iri. Ba zai zama adalci ba ga al’ummanmu idan muka takaita zabinmu a kan iya mutanen nan biyu ba.