Ba mu fushi kan faduwarmu a zabe ba – Farfesa Alkali

Farfesa Rufa’i Ahmad Alkali shi ne mai baiwa Shugaban kasa Jonathan shawara a kan al’amuran siyasa, Aminiya ta zanta da shi a kan yadda Jam’iyyar PDP ta ji kan sakamakon zaben da ya gabata dakomawarta matsayin jam’iyyar adawa a yanzu: Aminiya: An gudanar da zabubbuka ciki har da na Shugaban kasa wanda kake matsayin mai […]

Ba mu fushi kan faduwarmu a zabe ba – Farfesa Alkali
Ba mu fushi kan faduwarmu a zabe ba – Farfesa Alkali

Farfesa Rufa’i Ahmad Alkali shi ne mai baiwa Shugaban kasa Jonathan shawara a kan al’amuran siyasa, Aminiya ta zanta da shi a kan yadda Jam’iyyar PDP ta ji kan sakamakon zaben da ya gabata dakomawarta matsayin jam’iyyar adawa a yanzu:

Aminiya: An gudanar da zabubbuka ciki har da na Shugaban kasa wanda kake matsayin mai ba shi shawara a kan siyasa, yaya kuka ji da sakamakon zaben?
Farfesa Alkali: To mun gode wa Allah Mai kowa Mai komai, ana cewa za a yi zabe, za a yi zabe, ga shi Allah Ya nuna mana an yi zaben 2015 an gama lafiya, sai mu kara gode wa Allah da Ya nuna mana wannan lokaci, kuma Ya takaita mana matsalolin da kan biyo bayan zabubbuka.
Aminiya: Jam’iyyarku ta PDP ta yi ta kurarin za ta samu gagarumin nasara a zaben sai ga akasin hakan, me kake jin ya jawo mata faduwa?
Farfesa Alkali: Ka san dan Adam na nasa, Allah na naSa, dama ko a lokacin da muke yakin neman zabe ai ba mu ce, mu ne za mu ba kanmu nasara ba, mun dogara ga Allah ne, iyaka dama abin da dimokuradiyya ta gada ta koyar ta kuma saba a kai, shi ne ka nemi goyon bayan jama’a, hakan muka yi an yi kamfe daidai gwargwado, to tunda Allah Ya yi naSa hukuncin ai zai yi wuya kuma mutum ya ce zai yi fushi da hukuncinSa.
Aminiya: A baya Jam’iyyar PDP ta yi hasashen za ta shekara 60 a kan mulkin kasar nan, to, ga shi yanzu wannan abu ya fita a hanunta, za ku iya jurewa kuwa a matsayin ’yan adawa?
Farfesa Alkali: To, kamar yadda ka sani bayanin cewa jam’iyya za ta yi shekara da shekaru tana mulki, fata ne! Kuma fata ba laifi ba ne, ba wanda zai so ya yi wa mahaifiyarsa ko mahaifinsa fatar mutuwa, haka nan ba dan siyasar da zai yi wa jam’iyyarsa fatar gazawa ko lalacewa, saboda haka dole ne a bai wa jama’a azama a nuna masu hanya su bi. Saboda idan ka nuna musu cewa za ta rushe nan da shekara biyu to wane ne zai bi, wannan dai fata ne. Sai dai fa kada ka manta su wadanda suka yi nasarar a cikin wata jam’iyyar, ai yawancinsu ’ya’yan PDP ne, sauya sheka kawai suka yi. Ba sai an kai ka da nisa ba, idan ka dubi Sakkwato wanda ya ci zaben Gwamna a wurin Alhaji Aminu Tambuwal dan PDP ne, a Jihar Kebbi Sanata Bagudu ma dan PDP ne, in ka dubi na Katsina Masari dan PDP ne, ya yi Shugaban Majalisar Wakilai a jam’iyyar, a Kaduna Nasiru El-Rufa’i shi ma dan PDP ne ya yi Minista a karkashinta. A Adamawa Bindow dan PDP ne yanzu haka ma a kan kujerarta yake Sanata, na Benue Samuel Ortum dan PDP ne ya yi sakataren jiha na jam’iyyar, ya kuma yi Odita na kasa na PDP, a Jihar Taraba A’isha ita ma ’yar PDP ce ta kai Sanata, wannan dai na takaita maka ne kawai.
Aminiya: To bayan wadanda ka lissafo sun samu nasara a kan sun sauya sheka, sai ga shi har yanzu wasu na ci gaba da ficewa daga cikin jam’iyyar, hakan ba zai shafe PDP daga doron kasa ba musamman a nan Arewa”
Farfesa Alkali: Kowa yana da dalili ko manufa na shiga jam’iyya ko ficewa daga cikinta, ni ba zan yi magana a madadin wasu ba, illa iyaka kowa yana da buri ko manufa na kasancewarsa a jam’iyya, sai dai ka sani abin da ya ba ka mamaki an ce wata rana shi zai ba ka tsoro.
Aminiya: Kusan daukacin gwamnonin PDP ko a ce wadanda ta tsayar takara a nan Arewa sun sha kasa in ban da a jiharka ta Gombe, me kake jin ya kawo masa nasara?
Farfesa Alkali: To na hakikance shi ya tashi tsaye kuma tsayuwar daka, sannan ya dauki karin darasi daga yadda sakamakon zaben Shugaban kasa ya kasance, ya kuma samu goyon bayan ’yan jam’iyya ta kowane bangare.Na tabbata hakan ya kawo masa sassauci, kuma mu kanmu hakan zai kara mana darasi da za mu dauka musamman a zabubbukan jihohi da ke tafe, saboda akwai jihohi kamar bakwai da ba a yi zaben Gwamna ba, akwai Osun da Ekiti da Ondo da Edo da Anambra da Kogi, na tabbata dole a samu karin darasi game da su.
Aminiya: A karshe wani labari da ke kara-kaina a wannan mako shi ne wanda ake cewa Shugaban kasa ya bayyana rashin gamsuwarsa a kan yadda aka tafiyar da kudin kamfe kuma zai yi bincike a kai, yaya kuka ji wannan labara?
Farfesa Alkali: Mutane dama sun saba kitsa labari daga cikin dakunansu sannan Allah Ya ba su damar samun kafofi da suke yada labaran. Ribar dimokuradiyyar ke nan kowa na da hurumin fadin albarkacin bakinsa. Sai dai fa kada ka manta ya kamata kafin a yada labari abinciki sahihancinsa tukuna musamman ma idan zai shafi cin mutuncin wani ko wasu. Duk wanda zai ce maka za a kashe kudi kamar Naiara tiriliyan biyu a kamfe wanda ya kai matsayin daya bisa biyu na kasafin kudin Najeriya gaba daya, ai idan mai fadi ya zama mahaukaci bai kamata mai sauraro ya kasance mahaukaci ba. Abu na biyu kowa ya san cewa siyasa idan za ka yi al’amari ne na kasada da dole sai an yi asara a ciki, ashe zai yi wuya idan ba ka samu nasara a cikinta ba, ka ce za ka bukaci a mayar maka da abin da ka kashe. Idan wasu na yi to, ai ban ji Shugaban kasa zai yi hakan, inda zai yi tun farko da ba haka zai tafiyar da siyasarsa ba. Misali ka ga an ce bai ci zabe ba, amma cikin lokaci kankane ba tsangwama ba tursasawa ya ce ya amince da sakamakon zaben, ba don komai bai sai don kasa ta zauna lafiya. Ashe karrama shi ya kamata mu yi ba cin fuska ba, kamar yadda shi ma wanda zai shigo a yanzu zai so a yi masa. Ya shiga cikin sahun tsofaffin shugabannin kasa cikin halin lafiya. Kuma wannan ba tarbiyanmu ba ce ba kuma shi ne abin da za mu so mu koya wa na bayanmu ba.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi