Ba mu ga wani canji ba kan sake bude iyakokin Najeriya —Yahaya Kega
Shugaban Kungiyar masu sayar da motoci ta Najeriya, reshen Jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya ce har yanzu babu wani canji da suka gani sakamakon sake bude kan iyakokin Najeriya da Gwamnatin Tarayya ta yi kwanakin baya. A zantawarsa da Aminiya a garin Jos, Yahaya Kega wanda shi ne Shugaban Kamfanin sayar da motoci […]
Shugaban Kungiyar masu sayar da motoci ta Najeriya, reshen Jihar Filato, Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya ce har yanzu babu wani canji da suka gani sakamakon sake bude kan iyakokin Najeriya da Gwamnatin Tarayya ta yi kwanakin baya.
A zantawarsa da Aminiya a garin Jos, Yahaya Kega wanda shi ne Shugaban Kamfanin sayar da motoci na Kega Motors da ke garin Jos, ya ce halin da ake ciki kan sake bude kan iyakokin kasar nan, kamar murna tana neman ta sake komawa ciki.
- Kannywood ta zama kasuwar bukata – Zango
- Iyaye sun yi karar saurayin ’yarsu kan fasa auren ta
- Bom ya kashe sojoji 5, ya jikkata 15 a Borno
- Abubuwan da ya kamata ku sani game da yakin basasar Najeriya
Domin kowa ya yi farin ciki da jin labarin sake bude iyakokin kasar nan saboda rufe kan iyakokin ya kawo damuwa amma har yanzu tun da aka sake bude kan iyakokin, ba a ga wani canji ba.
“Har yanzu gwamnati, ba ta yi wani tsarin da zai nuna cewa an sake bude kan iyakokin ba, ta yadda za a nuna yadda kayayyaki za su rika shigowa kasar nan,” inji Alhaji Yahaya.
“Abin da muke so mu gani shi ne mu ga cewa an bude hanyar kasuwanci tsakanin kasa da kasa da makwabtanmu kamar Nijar da Kamaru da Benin da Chadi.
“Domin a lokacin da aka rufe kan iyakokin nan, abin ya shafi kowa da kowa a wadannan kasashe. Don haka rufe kan iyakokin nan ya kawo damuwa.”
Alhaji Yahaya Kega ya yi bayanin cewa, har yanzu an ce an sake bude kan iyakokin nan, amma har yanzu idan ka je wadannan kan iyakoki, yawancin abubuwa suna nan rufe kamar da.
Ya ce ya kamata tun da Shugaban Kasa ya ba da sanarwar cewa an sake bude kan iyakokin kasar nan, ya bi matakan sake bude kan iyakokin da aiki a gani. Ba wai a ce an sake bude kan iyakokin da baki ba.
Kega ya kara da cewa, akwai wadanda su ne suke kula da iyakokin nan, don haka ya kamata a nuna masu irin abubuwan da ya kamata su yi, na sake bude kan iyakokin nan.
A yi magana da jami’an Fasa Kwauri da sauran jami’an da suke kula da wadannan kan iyakoki a fada masu ga abubuwan da ake so su yi.
“Bude iyakokin nan ba wai zai tsaya ga shigo da kaya ne kawai ba. Mu ma za mu rika fitar da kayayyaki zuwa waje, kamar kayan noma da za mu rika fitarwa muna samun kudaden kasashen waje.
“Abubuwan da ba mu da su a shigo da su kamar motoci. Idan ana son talaka ya ji dadi a Najeriya, ya sami abin yi, dole a bari a rika shigo da motoci.”