Ba mu gamsu da zaben Bauchi ba, kotu za mu tafi – APC

Dan takarar ya yi zargin an tafka magudi a zaben Jihar

Ba mu gamsu da zaben Bauchi ba, kotu za mu tafi – APC

Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi ta yi watsi da sakamakon zaben Gwamnan da aka gudanar a Jihar ranar Asabar, wanda Gwamna Bala Mohammed na PDP ya sake lashewa.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Sanata Bala a matsayin wanda ya lashe shi bayan ya doke Iya Mashal Sadique Abubakar (mai ritaya) na APC.

Sai dai da yake jawabi ga manema labarai a Bauchi, Iya Mashal Sadique, ya ce zaben cike yake da tashe-tashen hankulan ’yan daba da cin zarafin ’yan adawa da kuma fitar da wakilan APC daga rumfunan zabe da dama a fadin jihar.

Sadique ya bayyana cewa, “Kwamishinoni da shuwagabannin Kananan Hukumomin Jihar sun dauki kusan dukkanin ayyukan zabe musamman a garin Bauchi inda aka ga Sakataren Gwamnatin Jihar yana ta yawo da Kwamishinoni da shugabannin Kananan Hukumomi daga wannan cibiyar zabe zuwa waccan tsawon dare, su watsar ko su fatattaki wakilan APC, a can suka karbe takardun suka rubuta abin da suke so su rubuta.

“Wannan ko kadan abin bakin ciki ne matuka, baya ga tursasa ’yan jam’iyyar APC da jami’an rumfunan zabe da na tattara kuri’u, mun kuma an samu tashe-tashen hankula a akalla Kananan Hukumomi bakwai.

“Saboda haka abin da ya zo daga Warji ba shi ne hakikanin abin da mutanen Warji suke so ba saboda an kirkiro alkaluma, an rubuta a takardu kuma abin da aka mika ke nan, abin bakin ciki ma an karbi wannan takardar,” in ji Sadique.

Ya kara da cewa, “Idan kuka zo Karamar Hukumar Toro kuma an yi tashe-tashen hankula a yankuna da dama domin a zahiri an jikkata jami’in tsaron farin kaya (DSS) kuma a halin yanzu yana asibiti.

“Muna yin kokari sosai don jawo hankalin hukumomin da abin ya shafa a kan abin da ke faruwa amma abin takaici ba ma sa duba da gaske kan al’amuran da suka shafi daukar matakin da ya kamata.”

Dan takarar Gwamnan ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankalinsu kuma kada su dauki doka a hannunsu amma su bar jami’an jam’iyyar su tuntubi sauran masu ruwa da tsaki don yanke hukunci kan mataki na gaba.

Daga karshe ya gode wa magoya bayansa bisa hakuri da juriyar da suka nuna a fadin Jihar musamman a yankunan da aka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.