Ba mu ji dadin hana shigo da motoci ba – Yahaya Kega
Shugaban kungiyar Masu Sayar da Motoci ta kasa reshen Jihar Filato kuma Shugaban Kamfanin Sayar da Motoci na Kega Motors da ke garin Jos, Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana cewa ba su ji dadin matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka ba na hana shigo da motoci ta kan iyakoki na kasa. Alhaji Yahaya Muhammad […]
Shugaban kungiyar Masu Sayar da Motoci ta kasa reshen Jihar Filato kuma Shugaban Kamfanin Sayar da Motoci na Kega Motors da ke garin Jos, Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana cewa ba su ji dadin matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka ba na hana shigo da motoci ta kan iyakoki na kasa.
Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya.
Ya ce a gaskiya mu masu sayar da motoci ba mu ji dadin matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na haramta shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan ba. Domin motocin da ake shigowa da su ta kan iyakokin Najeriya ana biyan kudaden fito su.
Har ila yau, ya ce kan iyakokin kasar nan, hanyoyi ne na shigo da kayayyaki don su wadata a cikin kasa kuma su yi sauki. “Yanzu an zo an ce an hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan, kamar yadda aka hana shigo da shinkafa. Wadannan abubuwa da gwamnati take yi a gaskiya tana kuntatawa al’ummar kasar nan, musamman mutanen arewa. Domin yawaicin harkokin da muka sanya a gaba ne ake takurawa. Wadannan abubuwa muna shigo da su domin mu samu taro da sisi ta hanyar kasuwancinmu. Su mutanen kudu suna da mai da tashoshin jiragen ruwa don haka suna da hanyoyin samun kudi. To dan wuraren da ake ci ake rage mana mu samu mu ci mu da iyalanmu da mutanen da suke karkashinmu ana ta bi ana kullewa,” inji shi.
Alhaji Yahaya Kega ya yi bayanin cewa a gaskiya ya kamata gwamnatin nan ta samu masu shawara nagari, domin wadanda suka kewaye shugaban kasa ba sa bashi shawarwari nagari kuma mutane ne masu son kansu kawai.
Ya ce kafin a zo a kafa wannan doka saboda matsalar tsadar canji ba a zuwa a sayo motocin nan sosai kamar yadda ake yi ada, domin kashi 20 cikin 100 ne suke iya fita su sayo motocin nan. Ya ce to yanzu da aka kawo wannan doka, kamar an kulle kofa ne kwatata.
Ya ce wannan mataki zai shafi masu sayar da motoci kuma zai shafi masu saye domin motocin za su kara tsada. Don haka ya kamata gwamnati ta sake tunani kan wannan mataki da ta dauka na hana shigo da motoci ta kan iyakokin kasar nan.