Ba mu ji dadin tallar da Gwamna Fayose ya sanya ba -Hukumar Kula da Tallace-tallace
Aminiya ta samu tattaunawa da Babban Daraktan Hukumar tallace-tallace na kasa (APCON), Garba Kankarofi jim kadan bayan kamfanin Media Trust masu buga jaridun Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da Kilimanjaro da Aminiya ya kaddamar da sabon injin buga jarida a yankin Ikeja da ke unguwar Oregun a Jihar Legas a ranar Alhamis […]

Aminiya ta samu tattaunawa da Babban Daraktan Hukumar tallace-tallace na kasa (APCON), Garba Kankarofi jim kadan bayan kamfanin Media Trust masu buga jaridun Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da Kilimanjaro da Aminiya ya kaddamar da sabon injin buga jarida a yankin Ikeja da ke unguwar Oregun a Jihar Legas a ranar Alhamis din da ta gabata. Ya yi bayani dangane da batutuwa da yawa wadanda suka hada da rashin bin doka da oda da wasu gidajen jarida suke yi dangane da tallace-tallacen da suke sanyawa da batun tallar da Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose ya sanya a shafin farko a wasu jaridu wanda ya janyo cece-kuce: Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ka yi batun cewa kamfanin Media Trust yana daya daga cikin kamfanonin da ke bin ka’ida dangane da sanya tallace-tallace a jaridunsu, me ya sa ka fadi haka?
Kankarofi: Abin da ya sa na yi wannan furuci shi ne cikin sauki za ka iya ganewa, idan gidan jarida ya saba doka ni da kai za mu gane, abu ne mai sauki su kansu masu karatu za su gane. Mu a matsayinmu na hukumar da ke kula da tallace-tallace a kafafen yada labarai, kullum muna bin diddigin abubuwan da jaridu suke bugawa na talla. Don a kullum mukan bi shafi-shafi mu ga tallace-tallacen da aka buga don mu tabbatar cewa kowace talla ta cika ka’idar da ta kamata. Duk wata tallar da ka sani a kasar nan in ban da talla a kan mutuwa ko sanarwa dole ne ya biyo ta ofishinmu. Kuma a kididdigar da muka yi kamfanin Media Trust shi ne yana bin ka’ida dangane da abin da ya shafi tallace-tallace a kasar nan. A shekaru biyu zuwa uku da suka gabata kamfanin Media Trust ya yi rawar- gani wajen bin ka’idar talla sau da kafa. Shi ya sa mu duk gidan jaridar da yake bin ka’ida da doka dole mu yaba masa. Yanzu idan ka je kasar Indiya ka buga talla mai dauke da kage daure ka za a yi. Su na da tsari ko da masu sayar da giya da sauran lemon kwalba da makulashe suna da ka’idoji. Amma a Najeriya muna da bangare biyu ne kawai, akwai bangaren kamfanonin dillancin tallace-tallace akwai kuma mu da muke bin diddigi tallace-tallace da aka buga. Shi ya sa muke son mu fito da sabon tsari irin na kasar Indiya don bunkasa harkar tallace-tallace a kasar nan.
Aminiya: Akwai tallar da Gwamnan Jihar Ekiti ya sanya a wasu jaridu, inda ya yi wasu maganganu kan dan takarar jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari, ya hukumar APCON ta ji a lokacin da wasu jaridu suka buga wannan tallar?
Kankarofi: Gaskiya ba mu ji dadi ba. Ka san mu a matsayinmu na hukumar APCON muna da iyakar da doka ta yi mana. Hukumar ’yan Jarida ta kasa wato Nigerian Press Council ita ya kamata ta dauki mataki kan batun. Ni abin da na yi shi ne na rubuta takardar tuhuma ga kamfanin jaridar da ya sanya tallar kuma na yi abin da ya dace. Abin da na tambaya shi ne, me ya sa wasu ’yan Najeriya suke karbar irin wadannan kudin badakala. Idan ka lura za ka ga ita kanta jam’iyyar PDP ta nisanta kanta daga abin da gwamnan ya yi. Ka ga ni dan Najeriya ne, an haife ni a Jihar Kano amma na girma a yankin Kudu. Na yi kusan shekara 40 a Jihar Legas. Idan na tafi Jihar Ondo ko garin Abeokuta ina da aboki da zan je wurinsa. Ni dan Najeriya ne na ainihi. To idan haka ne, me zai sa wani yake kokarin dakushe wannan kasa tamu ta Najeriya. Me zai sa wani ya rika bayyana son ransa ga ’yan Najeriya. Ka lura baki daya, mu ’yan’uwan juna ne. Saboda haka abin da mai girma Gwamna Fayose ya yi ba mu amince da shi ba. Mun rubuta takadar tuhuma ga jaridar, ya rage ga gwamnati ta dauki matakin da ya dace a kan lamarin. Kodayake ka ji martanin da ’yan Najeriya suka rika mayarwa kan lamarin.
Aminiya: A matsayinku na masu tabbatar da an bi ka’ida a harkar tallace-tallace a kasar nan, wane mataki za ku dauka a kan Gwamna Fayose?
Kankarofi: Ba hurunmu ba ne mu hukunta shi. A matsayinmu na hukumar APCON ba mu da wani lamari game da shi don doka ta yi mana iyaka. Doka ba ta ba mu damar mu rufe gidan jaridar ba, ita kanta cibiyar ’yan jarida ta kasa ba ta da damar rufe gidan jaridar. Wannan wani batu ne da ake takaddama a kansa, tsakanin cibiyar ’yan jarida ta kasa da hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa ta NBC. Har sai an gyara dokokin hukumar NBS, sannan za a iya magani irin wadannan abubuwan da ba su dace ba a gidan jaridu. Bari in gaya maka ko wane ne editan jaridar bai yi wa kasar nan abin da ya dace ba. Kamar yadda ka sani tallar da Gwamna ya sanya ya janyo kace-nace a kafafen yada labarai, kuma ya zama wani abin tattaunawa a wasu gidajen talabijin kamar gidan talabijin na NTA da sauran gidan jaridu na kasar nan.
Aminiya: Ka ce kun rubuta takardar tuhuma ga kamfanin dillancin tallar da ya jagoranci sanya tallar Gwamnan Jihar Ekiti, shin za ka yi karin haske dangane da wannan batu?
Kankarofi: Saboda doka ta yi mini iyaka shi sa abin da zan iya kawai shi ne in rubuta takardar tuhuma ga kamfanin dillancin tallar da kuma gidan jaridar, kuma mun fitar da matsayarmu a kan batun a madadin hukumar APCON. Ya rage ga gidajen jarida su dauki mataki na bin ka’ida kamar yadda hukumar APCON ta tsara. Ya kamata mu rika lura, mu rika yi wa kanmu tambaya kafin mu sanya talla cewa, shin tallar da za mu sanya a kafafen yada labarai, shin ya dace da doka? Kuma shin zai harfar da da mai ido ga ’yan Najeriya da ita kanta Najeriyar? Ka ga duk abin da zai faru ba ni da wata kasa sai Najeriya babu inda zan je saboda ina da zuri’a da ’yan’uwa da abokan arziki. Ina da wani baffana da ya sadaukar da kansa ga Najeriya a yake-yake da dama a ciki da wajen kasar nan, wanda a sakamakon haka a yanzu yana fama da rashin lafiya har ma ba ya iya tafiya, kullum yana kan keken guragu, kuma ni nake kula da shi a yanzu, don shi ya raine ni, ka ga ba zan tafi na kyale shi ba. Saboda haka ka ga akwai gidajen dillancin talla da suke karbar talla ba tare da lura da irin wadannan abubuwa ba. Shi ya sa nake tabbatar maka da cewa mutum kamar Gwamna Fayose yana da dangi a Jihar Imo da Kano da Sakkwato, dole ya zama yana da dan’uwa a wadannan yankunan don dole a samu auratayya a tsakani. Shi ya sa nake cewa ba yadda za a iya raba wannan kasa, ba zai yiwu ba. Duk abin da zai faru dole mu ci gaba da kasancewa ’yan Najeriya tsintsiya madaurinki daya. Idan ka je Togo ko kasar Ghana za su koro ka. Saboda haka ina mai tabbatar maka da cewa a matsayina na dan Najeriya ina da ’yancin na ce ban amince da tallar ba.