‘Ba mu ji dadin watsi da makarantar nakasassu ta Yobe ba’
Tsohon Shugaban Makarantar Nakasassu ta Jihar Yobe, Malam Ibrahim Bukar Goneri ya koka kan yadda gwamnatin jihar ta daina kula da makarantar. Malam Ibrahim Goneri, ya yi wannan koke ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Kano, lokacin taron kara wa juna sani kan makomar nakasassu, inda ya ce a da makarantar tana garin […]

Tsohon Shugaban Makarantar Nakasassu ta Jihar Yobe, Malam Ibrahim Bukar Goneri ya koka kan yadda gwamnatin jihar ta daina kula da makarantar.
Malam Ibrahim Goneri, ya yi wannan koke ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Kano, lokacin taron kara wa juna sani kan makomar nakasassu, inda ya ce a da makarantar tana garin Goneri ne amma yanzu an dawo da ita Damagum kuma an kafa ta ce a ranar 6 ga Satumban shekarar 2004.
Ya ce makarantar yanzu haka babu kayan aiki, ba wani abu da gwamnati take yi ga makarantar illa ciyarwa, wanda hakan ya jefa makarantar a cikin ci bayan da take ciki a yanzu.
A cewar tsohon shugaban makarantar, “Yanzu malaman da ke koyar da ilimi na musamman guda uku ne kadai, daga shugaban makarantar sai wadansu malamai biyu. Ta yaya za su iya koyar da kurame da makafin da suke makarantar?”
Ya ce yanzu haka ajujuwan karatunsu nan ne kicin din da suke girke-girke, dakunan kwanansu kuma nan ne ajujuwan karatu.
Goneri ya ce makarantar tana matukar bukatar taimakon gwamnati wajen gyara ta da samar mata da kayayyakin aiki irin na masu nakasa, musamman keken rubutu na makafi da abin rubutu na kurame. Sannan ya ce kukan da suke yi na yin karatu na musamman irin na masu nakasa ma ba a inganta shi ba, ina kuma ga tsarin karatu na bai-daya da wadanda ba su da nakasa?
Daga nan sai ya yi kira ga kungiyoyi da hukumomi su kai musu dauki wajen ganin an ceto makarantar daga halin da take ciki.