Ba mu ji dadin zama da El-Zakzaki ba – Mutanen Gyallesu

Wadansu mazauna Gyallesu da ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna sun faiyyace irin zaman kuncin da sukayi tare da Malam Ibrahim El-Zakzaki, inda  wani mazaunin layin Sarkin yaki mai suna Malam Muhammadu Sani, ya ce ‘Akalla shekar na Sitin da daya kuma a nan Unguwar aka haife ni kuma tsakanina da gidansa babu nisa, […]

Ba mu ji dadin zama da El-Zakzaki ba – Mutanen Gyallesu
Ba mu ji dadin zama da El-Zakzaki ba – Mutanen Gyallesu

Wadansu mazauna Gyallesu da ke karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna sun faiyyace irin zaman kuncin da sukayi tare da Malam Ibrahim El-Zakzaki, inda  wani mazaunin layin Sarkin yaki mai suna Malam Muhammadu Sani, ya ce ‘Akalla shekar na Sitin da daya kuma a nan Unguwar aka haife ni kuma tsakanina da gidansa babu nisa, kuma filin da al’majiransa suke taruwa ko suke aje abin hawansu yana jikin gidana ne. Wato mu makwabtansa ne, sai dai mun kasance kamar muna gidan kaso, ko wani ziri wanda ba ya karkashin hukumar Najeriya, domin babu inda za ka kai kara idan wani abu ya hada ka da shi ko al’majiransa, kasancewar ya maida kansa hukuma mai zaman kansa, domin dokoki ne aka shimfida mana iri-iri a Unguwar, ga kuma shingaye da al’majiransa suka kakkafa mana a ko’ina, idan ka fito daga gida da yarinyarka ko da ‘yar shekara biyu ce sai an caje ta, haka ma ‘ya‘yanmu mata da kuma matanmu da muke aure duk sai an caje su, motarka ita ma sai an duba ko’ina kullum idan ka dawo, duk da sun sanka, ballantana a ce ka yo dare, wai da sunan suna tsare Malam.’’
‘A  ranar 9 ga watan Mayu na shekarar da ta gabata suka taru a kofar gidana da daddare suka ce in fito musu da dana, ashe ba mu sani ba  sun yanke masa hukuncin kisa ne tare da sauran wadansu fiye da 30, wai sun sa sunayensu a bakin littafi  (Black list) kuma lafinsu sun ki yarda a caje su a wajen shingayensu ko kuma ba sa ba su hadin kai. Kamar yarona wai laifinsa yana gudu a kan abin hawa, don haka ne aka yanke masa hukuncin kisa, shi ne aka zo in ba da shi. Duk da su ma suna da irin manyan baburan nan wanda idan Malaminsu ya fito sukan tattare hanya suna jan adduna a kasa kuma a wannan lokaci idan sun fito duk wanda suka bige sun bige banza, banlantana tsautsayi ya gitta abin hawanka ya mutu ko kuma kana kokarin kaucewa, sai su tsaya su fito da kai a cikin motarka su ba ka kashi kuma su farfasa maka mota, babu abin da zai faru, domin babu inda za ka kai kara.’’
Ya ci gaba da cewa, ‘Ana cikin haka sai suka kewaye gidana suka fara dukan kofar gidan, ni kuma sai na umurci yarona da ya haura makwabta domin ya bulla ta can ya gudu, domin a lokacin har sun kashe wani yaro mai suna Ibrahim, wanda dan Unguwa ne, kuma sauran yaran da suka yanke wa hukuncin kisan duk sun tsere, haka suka shigo cikin gidana daki-daki suna neman wannan yaro, a kan haka daya daga cikinsu ya sare ni da adda, wani mai suna Musa Sabo da Kaza ba ya hana yanka, wani mutumin Faskari, domin duk wadannan mutane babu ‘yan Gyallesu ko daya, haka kuma yawancin ‘yan taurin daga Kura ta jihar Kano aka zo da su da manyan karnukansu suna hura kaho, haka muka kasance na tsawon makonni biyu kafin Allah Ya kawo mana wannan dauk,i domin mu Allah ne Ya yi mana wannan, ba wai sojoji ba.’
‘Akwai lokacin da marigayi tsohon Ministan man fetur Dokta Rilwanu Lukuman ya zo gaida dan uwansa saboda ba shi da lafiya, shi ma suka ce wai sai dai ya sauka ya taka da kafarsa, an samu cacar baki kafin ya wuce, mutanen Unguwar nan ma sun nuna bacin ransu. Akwai wani babban sojan ruwa mai mukamin Riya Adimiral, mai suna Tahir Y. Biu, wanda da ne da Gyallesu ke alfahari da shi, wanda ya ziyarci iyayensa da ‘yan uwansa,  shi ma ya zo da tawagar motocinsa suka hana shi shiga, ba don an kai hankali nesa ba da tun a lokacin ta-baci. To ka ji irin cin mutuncin da suka rika yi mana a wannan Unguwa tamu.’
‘Domin a baya sun hana mai girma tsohon gwamnar jihar Kaduna Dokta Muktar Ramalan Yero shiga Unguwar lokcin da ya zo gai da mara lafiya, wai sai dai ya sauka ya tafi a kasa ba tare da jami’an tsaro ba, kuma haka aka yi, ya taka har inda za shi, wannan ya haifar da bacin ra,i a inda matasa suka hassala suka je suka cire duk wata kofa ta shiga Gyallesu.’
Sakataren mazauna Unguwar, Gyallesu mai suna Bilyaminu Muhammed Ahmad, cewa ya yi ‘tsaronmu ya faro asali ne daga lokacin da wasu  gungun  ‘yan fashi suka shigo suka kashe mana wani jagoran Unguwa mai suna Alhaji Buba, tun daga lokacin muka dauki matakin tsaron Unguwa, don haka tun kafin Malam ya zo muna da tsari a Unguwar na tarbiyya tare da bin dokoki da ka’idoji na zamantakewa, domin haka Malam ya same mu da tsarinmu, a lokacin muka kirkiri yin shigaye a hanyoyin shiga Unguwarmu, a wannan lokaci zamantakewarmu da shi bai gurbata sosai ba, domin har gudummawa ya bayar a lokacin da ake sa shingen shiga layin Madaki da aka yi, sauran mashigin Uguwar kuwa wadansu dattawan Unguwa suka dauki nauyin sa kofofin.’
‘Malam ya shigo Unguwan Gyallesu ne a karshen shekarar 1998, bayan sako shi da tsohon shugaban kasa Abdulsalam ya yi daga gidan kaso a sanadiyyar kama shi da tsare shi da tsohon shugaban kasa Sani Abacha ya yi, tun daga wancan lokaci al’majiransa suka taru domin taya shi murnar dawowarsa daga gidan kaso, ba tare da neman izinin jami’an tsaro ba, inda jami’an tsaron suka shigo Unguwar domin tarwatsa su, wannan ya  haifarda shiga matsalarmu ta farko, saboda irin yadda jami’an ‘yan sandan suka rika amfani da barkonon tsohuwa (tiya gas) wanda ya yi sanadiyyar wani wanda ba al’majirinsa ba mai sana’ar sai da dabino ya rasa ransa, tun daga wannan lokacin muka fara fuskantar matsala da shi.’
‘Idan muka samu matsala da al’majiransa mukan koka wa hakiminmu domin a tsawatar, hakimin yana kokari domin taro masu Unguwanni da dagatansa da dattawan Unguwa tare da matasa masu hankali, su kuma akan nemi da su zo domin a samu mafita amma duk taron da muke yi bai taba talarta ba, sai dai wakilci, kai idan abin ya baci sai dai hakimin ya jagoranci wasu daga cikin mazauna Unguwar a je wurinsa domin nema masalaha, kuma duk yarjejeniyar da aka yi bayan awa biyar sai ka ga sun saba.’
Ya kara da cewa, ‘Bayan haka, mun sha zama tare da wakilan tsaro da wakilin masarautar zazzau, akalla zai kai sau 15, kuma mun je gaban Mai martaba sau daya, a zaman da muka yi da shi ya ba mu hakuri ya ce mu zama masu bin doka da kuma oda, kuma mu lallashi al’ummarmu da su zauna lafiya, idan Allah Ya yarda za su duba koke-kokenmu, hakan dai bai samu ba har sai yanzu da Allah Ya kawo mana karshen wannan zaman na kunci da rashin ‘yanci na tsawon shekara 17.