Ba mu karbi kyautar Naira miliyan 10 daga Ganduje ba- EFCC

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta musanta rahoton da ke cewa, ta karbi kyautar Naira miliyan 10 daga hannun Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje don gudanar da taron yaki da cin hanci da rashawa. Hukumar EFCC ta ce, ba ta karbi ko kwabo daga hannun wani ko kungiya […]

Ba mu karbi kyautar Naira miliyan 10 daga Ganduje ba- EFCC

Dakataccen Shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati ta musanta rahoton da ke cewa, ta karbi kyautar Naira miliyan 10 daga hannun Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje don gudanar da taron yaki da cin hanci da rashawa.

Hukumar EFCC ta ce, ba ta karbi ko kwabo daga hannun wani ko kungiya ba saboda yasabawa ka’idan aikin hukumar karbar tallafin kudi daga Gwamnoni.

Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na Twitter @officialEFCC