Ba mu karkatar da tallafin Gwamnatin Tarayya ba – Gwamnatin Nasarawa
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta musanta jita-jitar da wasu a jihar ke yadawa cewa tana amfani da tallafin kudi da ta samu daga Gwamnatin Tarayya don biyan ma’aikatanta albashi wajen gudanar da wasu manyan ayyuka a jihar. Akanta Janar na Gwamnatin Jihar Alhaji Muhammed Musa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu […]
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta musanta jita-jitar da wasu a jihar ke yadawa cewa tana amfani da tallafin kudi da ta samu daga Gwamnatin Tarayya don biyan ma’aikatanta albashi wajen gudanar da wasu manyan ayyuka a jihar.
Akanta Janar na Gwamnatin Jihar Alhaji Muhammed Musa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke Lafiya, inda ya ce “Abin mamaki ne sosai a wajena don a yanzu da muke magana da kai wannan tallafin daga Gwamnatin Tarayya bai shigo asusun gwamnatin jihar nan ba. Muna kokari mu ga mun karbo kudin ne har yanzu. Na biyu kuma na tabbata cewa mai gidana Gwamnan Umaru Tanko Al-Makura mutum ne mai adalci da tsoron Allah, ba zai taba yarda ya yi amfani da tallafin kudin wajen gudanar da wasu ayyuka na daban ba idan suka zo. Wannan tallafi da jihohi da dama suka karba kamar yadda aka sani za a yi amfani da shi ne wajen biyan ma’aikata albashinsu. Babban Bankin Najeriya da ke bayar da kudin ya bayar ne da sunan biyan ma’aikatan jihohin albashinsu sakamakon gazawar da jihohin suka yi wajen biyan albashinsu na watanni. Kuma da zarar wannan kudi ya shigo asusunmu za mu yi amfani da shi yadda ya kamata.”
Sai ya bayyana jita-jitar a matsayin mara tushe, inda ya bukaci al’ummar jihar su kara hakuri har a kai ga biyan bukata.
Babban Akantan ya kuma ce, jihar tana cikin jihohin da suka bukaci bashin Naira biliyan 10 daga Babban Bankin Najeritya domin gudanar da wasu manyan ayyuka. Ya ce wannan Naira biliyan 10 ba ta da alaka da tallafin Gwamnatin Tarayya. “Amma abin mamaki har an fara yada jita-jita cewa muna amfani da kudin tallafi wajen gudanar da wasu manyan ayyuka a jihar nan,” Ya yi kira ga al’ummar jihar su yi watsi da jita-jitar, kuma ya tabbawar da cewa da zarar kudin sun shigo asusun gwamnatin jihar za a yi amfani da su yadda ya kamata.