Ba mu kashe ’Yan Boko Haram 250 a Maiduguri ba- Rundunar Soji

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta musanta rahoton rahoton bogi da ake yadawa cewa, sun kashe sama da 250 mayakan Boko Haram a Maiduguri babban birnin jihar Borno. Daraktan hulda da jama’a kuma jami’in watsa labarai na rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola, ne ya fitar da sanarwar ranar Lahadi, inda ya ce wannan rahoton bogi […]

Ba mu kashe ’Yan Boko Haram 250 a Maiduguri ba- Rundunar Soji

Rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ta musanta rahoton rahoton bogi da ake yadawa cewa, sun kashe sama da 250 mayakan Boko Haram a Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Daraktan hulda da jama’a kuma jami’in watsa labarai na rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola, ne ya fitar da sanarwar ranar Lahadi, inda ya ce wannan rahoton bogi ne da baida asali daga rundunar.

A ranar 13 ga Fabrairu 2020 ne Aminu Shuaibu Musawa, ya fitar da sanarwar kisan mayakan Boko Haram din da aka yi.