Ba mu kori Kocin U-17 Manu Garba ba – NFF
Sakatare Janar na Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF), Dokta Muhammad Sanusi, ya musanta rade-radin da wadansu ke yadawa cewa an kori Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta ’Yan kasa da shekara 17 da aka fi sani da Golden Eaglets, Manu Garba. Jim kadan da Holland ta fitar da Najeriya a gasar cin Kofin Duniya na […]
Manu Garba
Sakatare Janar na Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa (NFF), Dokta Muhammad Sanusi, ya musanta rade-radin da wadansu ke yadawa cewa an kori Kocin Kungiyar Kwallon Kafa ta ’Yan kasa da shekara 17 da aka fi sani da Golden Eaglets, Manu Garba.
Jim kadan da Holland ta fitar da Najeriya a gasar cin Kofin Duniya na ’yan kasa da shekara 17 da yanzu ke gudana a Brazil, sai wadansu suka shiga kafofin sada zumunta suka rika yada labarin cewa Hukumar NFF ta sallami Manu Garba a matsayin koci.
Dokta Sanusi ya fadi a ranar Talata cewa ba haka kawai ake korar koci ba sai an bi matakai. “Yanzu matakin da muke kai shi ne muna jiran kocin ya gabatar mana da cikakken rahotonsa game da gasar, daga nan ne za mu san matakin da za mu dauka. Zancen an kori Manu Garba daga kocin kungiyar karya ce,” inji shi.
’Yan Najeirya da dama ba su ji dadin yadda aka fitar da kungiyar a gasar ba, ganin ta yi wasanni biyu na farko da kafar dama amma a zagaye na biyu aka yi mata kifa daya kwala.
Najeriya ce ta fi yawan lashe gasar a tarihi, inda ta dauki kofin har sau biyar.