Ba mu kori Sanata Bala Na-Allah ba – APC
Jam’iyyar APC reshen Jihar Kebbi ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ta kori Sanata Bala Ibn Na-Allah daga jam’iyyar.Kakakin Jam’iyyar APC na Jihar Alhaji Sani Dodo ne ya bayyana haka a masaukin Shugaban kasa da ke Birnin-Kebbi, a wani taron manema labarai da jam’iyyar ta kira.Alhaji Sani Dodo ya ce, irin wadannan maganganu da […]
Jam’iyyar APC reshen Jihar Kebbi ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa ta kori Sanata Bala Ibn Na-Allah daga jam’iyyar.
Kakakin Jam’iyyar APC na Jihar Alhaji Sani Dodo ne ya bayyana haka a masaukin Shugaban kasa da ke Birnin-Kebbi, a wani taron manema labarai da jam’iyyar ta kira.
Alhaji Sani Dodo ya ce, irin wadannan maganganu da rubuce-rubuce da ake yi a kafafen sadarwa na Intanet kamar facebook ’yan Jam’iyyar PDP ne suke haddasa su domin kawo rudani a cikin Jam’iyyar APC.
Kakakin Jam’iyyar ya ce su a saninsu a matsayinsu na shugabannin APC a ba Sanata Bala Na-Allah ba mutum daya tun daga gundumomi zuwa kananan hukumomi da jiha da suka kora daga APC.
Alhaji Sani Dodo ya ce, Shugaban APC na mazabar Sanata Bala Na-Allah da shugabanta na karamar Hukumar Sakaba inda ya fito duk sun musanta wannan labarai marar tushe, saboda haka ya yai kira ga ’yan PDP na Jihar Kebbi su guji shiga cikin harkokin Jam’iyyar APC, saboda APC ba kamar PDP ba ce wadda ta saba kirkiro karya ba gaira ba dalili.
Alhaji Sani Dodo ya ce daga ranar da aka zabi Sanata Abubakar Atiku Bagudu a matsayin Gwamnan Jihar, Jam’iyyar PDP a jihar ta yi musu karya har guda shida, kuma al’ummar jihar sun sani.
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin Jam’iyyar PDP na Jihar Kebbi, Alhaji Ibrahim Ummai a kan wannan zargin da APC ke musu, ya ce APC kame-kame kawai take yi domin ta dauki alkawura a lokacin yakin neman zabe amma a cikin wata bakwai ta gaza sauke ko guda daya.
“Saboda haka fitintunun da ke cikin APC ya ishe su, su bar sanya PDP a ciki, kuma kowa ya san Sanata Bala Na-Allah yana da matsala da jama’arsa ko su suna iya shiga cikin facebook su rubuta cewa APC ta kore shi daga cikinta, tunda APC ta ce a cikin facebook ta gani ba kuma adireshin PDP suka gani, ba kuma sunan dan PDP ba,” inji shi.