Ba mu san amfanin Kungiyar Dattawan Arewa ba –’Yan Arewa mazauna Kudu
Kalaman da daya daga cikin shugabannin Kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya yi a wasu kafafan yada labarai a kwanakin baya cewa kungiyar ba za ta goyi bayan kudirin sake tsayawar takara na Shugaba Buhari ba, ’yan Arewa mazauna Kudu sun ce ba su san amfanin Kungiyar Dattawan Arewar ba. Kwamared Ya’u Musa Sakaba […]
Kalaman da daya daga cikin shugabannin Kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi ya yi a wasu kafafan yada labarai a kwanakin baya cewa kungiyar ba za ta goyi bayan kudirin sake tsayawar takara na Shugaba Buhari ba, ’yan Arewa mazauna Kudu sun ce ba su san amfanin Kungiyar Dattawan Arewar ba.
Kwamared Ya’u Musa Sakaba jagoran Kungiyar Matasan Arewa (NNYO) reshen jihohin Kudu maso Yamma ne ya shaida wa Aminiya haka, inda ya ce su al’ummar Arewa mazauna Kudu ba su san amfanin Kungiyar Dattawan Arewar ba, ko amfanin Farfesa Ango Abudullahi ba, domin ba su taba tsinana musu komai ba, don haka ba su dauki matsayar da suka yi na nuna kin jinin Shugaba Buhari da muhinmmanci ba. Ya ce sau tari ’yan Arewa mazauna Kudu kan fada mummunan hali na matsalolin zamantakewa, amma Kungiyar Dattawan Arewar ba ta taba tsinana musu komai ba. “Don haka ba mu dauke su da muhimanci ba, kuma mun yi tir da matakin da suka dauka a kan Shugaba Buhari, ba ma tare da su a wannan matsaya domin mu Shugaba Buhari shi ne zabinmu,” inji shi.
Ya ce kamata ya yi masu kiran kansu dattawa su rika nuna halin dattaku su kuma kyale jama’a su bi zabin da ya dace da su, ba su fito suna magana da yawun al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba. “Mu ba da yawunmu suka zartar da wancan kudiri ba, kamata ya yi dattawa su rika nuna dattaku, mu ’yan Arewa mazauna Kurmi muna tare da Shugaba Buhari dari bisa dari,” inji shi.