Ba mu san an kama ’yan ta’adda sun dawo daga aikin Hajji ba — Gwamnatin Katsina
Kwamishinan Yada Labarai da Raya Al’adu na Jihar Katsina, Bala Salisu Zango, ya shaida wa wakilinmu cewa ba shi da masani kan kama jagororin ’yan ta’addan a jihar.
Taswirar Jihar Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ba ta da abin cewa game da rahoton kama wasu jagororin ’yan ta’adda a yayin da suke dawowa daga aikin Hajjin bana a Filin Jirgin Sama da Umaru Musa Yar’Adua da ke jihar.
Aminiya ta ruwaito Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya sanar cewa a ranar Alhamis, 18 ga watan Yuni, 2026, jami’an tsaro sun kama wasu kwamandojin kungiyar ISWAP inda aka mika su ga hukumar tsaro da DSS.
Ministan ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi a Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan Dokar Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) ta shekarar 2026.
“Ina farin cikin sanar da ku cewa a makon da ya gabata, ranar Alhamis (18 ga Yuni, 2026), an kama shugabannin Boko Haram da ISWAP bakwai a filin jirgin Katsina lokacin da suke dawowa daga aikin Hajji, kuma an mika su ga Hukumar DSS,” in ji Ministan.
- ’Yan bindiga sun dasa bam a hanyar Sakkwato, sun kashe mutum ɗaya
- BUA ya bai wa manoma tallafin kayan noma na N100m a Sakkwato
- Da sana’ar sayar da ƙosai mahaifiyata ta raine ni — Hadimin Tinubu
Ko da yake bai bayyana sunayen wadanda aka kama ba, ko wanda ya dauki nauyin tafiyarsu zuwa aikin Hajji, ko da fasfo din wace kasa suka yi tafiyar da kuma yadda har aka tantance su, suka samu tafiyar, duk da cewa jami’an tsaro na neman su ruwa a jallo.
Ministan ya kara da cewa, tsarin tantance shaidar ɗan ƙasa na zamani ya taimaka wajen gano shugabannin ’yan ta’addan. A cewarsa, hakan ya isa zama shaida a kan ingancin sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa a fannin tantance shaidar ɗan ƙasa da tsaron iyakoki.
Ba mu da ta cewa — Gwamnatin Katsina
Da yake mayar da martani kan rahoton da ministan ya bayar, Kwamishinan Yada Labarai da Raya Al’adu na Jihar Katsina, Bala Salisu Zango, ya shaida wa wakilinmu cewa ba shi da masani kan kama jagororin ’yan ta’addan a jihar.
“Ba ni da labarin cewa an kama wani shugaban ’yan bindiga a hanyarsa ta dawowa daga aikin Hajji daga Kasar Saudiyya,” in ji shi.
Shi ma kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu Danmusa, ya bayyana cewa lamarin gaba daya hurumin hukumomin Gwamnatin Tarayya ne.
A hirar da BBC Hausa da kuma wakilinmu, Danmusa ya bayyana cewa ba Gwamnatin Jihar Katsina ba ce ta bayar da umarni ko ta aiwatar da kama wadanda ake zargin.
“Hukumomin Gwamnatin Tarayya ne ke kula da wadannan batutuwan tsaro da gudanarwa. Gwamnatin jihar ba ta hurumin tabbtarwa ko musa maganar kamen.
“Ya kamata ’yan jarida su tuntubi Hukumar Kula da Shige da Fice da kuam DSS domin samun hakikanin bayanai,” in ji shi.
Ya bayyana cewa kula da iyakokin kasa da tantance matafiya da kula da leken asiri ayyuka ne da hurumin gudanar da su ya kebanci hukumomin Gwamnatin Tarayya.
Duk da matsayar gwamnatin jihar da ta bayyana kan lamarin, rahoton ya ci gaba da haifar da muhawara a tsakanin al’ummar jihar, inda waduk ke danganta shi da zargin da ake cewa wasu shugabannin ’yan bindiga sun tafi aikin Hajjin bana ta hannun Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Katsina.
Wani fitaccen mai sharhin harkokin siyasa daga Jihar Katsina, Dakta Bashir Kurfi, a yayin hirarsa da shirin Daily Politics na gidan talabijin na Trust TV, ya yi zargin cewa gwamnatin jihar ta biya wa wasu gawurtattun ’yan bindiga da shugabannin kujerun aikin hajjin baya.
A cewarsa, “Abin tashin hankali ne muke gani. Gwamnantin Jihar Katsina ta dauki nauyin ’yan ta’adda zuwa aikin Hajji, cikinsu har da wani mai suna, Monore. Wannan ya sanya alamar tambaya game da tsarin tantance matafiya,” Kurfi.