Ba mu tsayar da Buhari shi kadai ba-Jam”iyyar APC
Jam’iyyar APC ta jinkirta amincewa da takarar shugaba Muhammdu Buhari a zaben shugaban kasa na shekarar 2019. Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ne ya sanar da haka yayin da yake yi wa manema labarai jawabi dangane da taron shugabannin jam’iyyar da ya gudana a Abuja jiya. Dogara wanda Sakataren Yada Labarai Na Jam’iyyar, Malam Bolaji […]

Jam’iyyar APC ta jinkirta amincewa da takarar shugaba Muhammdu Buhari a zaben shugaban kasa na shekarar 2019.
Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ne ya sanar da haka yayin da yake yi wa manema labarai jawabi dangane da taron shugabannin jam’iyyar da ya gudana a Abuja jiya.
Dogara wanda Sakataren Yada Labarai Na Jam’iyyar, Malam Bolaji Abdullahi da Lauyan Jam’iyyar Na Kasa, Dokta Muiz Banire suka rufa wa baya ya yi furucin ne a lokacin da aka tambaye shi ko shugabannin jam’iyyar sun amince da Buhari ya sake tsayawa takara a zabe mai zuwa.