Ba mu tsoron wargajewar Najeriya – Lamidon Adamawa … Taron kasa ya hadu da cikas

Mai martaba Lamidon Adamwa Alhaji Muhammadu Barkindo Mustapha ya ce Arewa ba ta tsoron wargajewar Najeriya, don haka sauran sassan kasar na su daina yi wa yankin wata barazana.Alhaji Muhammadu Barkindo Mustapha ya bayyana haka ne a wurin taron kasa, inda ya ce galibin mutanen da suke jawo mafi yawan matsalolin kasar nan su ne […]

Ba mu tsoron wargajewar Najeriya – Lamidon Adamawa … Taron kasa ya hadu da cikas

Mai martaba Lamidon Adamwa Alhaji Muhammadu Barkindo Mustapha ya ce Arewa ba ta tsoron wargajewar Najeriya, don haka sauran sassan kasar na su daina yi wa yankin wata barazana.
Alhaji Muhammadu Barkindo Mustapha ya bayyana haka ne a wurin taron kasa, inda ya ce galibin mutanen da suke jawo mafi yawan matsalolin kasar nan su ne wadandaba su da inda za su je idan ta wargaje.
Lamidon Adamawan wanda ya bayyana haka shekaranjiya a wurin zaman taron ya bukaci shugaban taron ne ya ba shi dama ya yi tsokaci kan halayyar wasu wakilan taron.
Ya yi gargadin cewa idan wadannan mutane suka ci gaba da irin wannan hali, mutane irinsa za su kaurace wa taron, “Idan aka kai mu bango za mu kaurace wa wannan taro,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Idan wani abu ya faru kasar nan ta wargaje Allah Ya kiyaye, galibin masu daga kai za su rasa inda za su je.”
Ya ce, “Amma ni da mutanen Adamawa da sauransu muna da wurin zuwa. Ni ne Lamidon Adamawa kuma masarautata ta tsallaka zuwa wajen Najeriya da Kamaru, kuma wani bangare na masarautar yana Jamhuriyar Chadi.
A shekaranjiya Laraba an samu cikas a taron bayan da Kwamitin Samar da Daidaito mai wakilai 50 ya kasa cimma matsaya kan fasalin yadda za a kada kuri’a a wurin taron.
An dai daga jijiyar wuya a zaman kwamitin na ranar Litinin da Talata kan yadda ya kamata a kada kuri’a lamarin da ya kawo rabuwar dakin taron zuwa Kudu da Arewa.
Da aka zauna ranar Talata sai dakin taron ya kaure da yi wa juna tsawa a tsakanin wakilai inda shugaban taron Mai shari’a Idris Kutigi ya dage zaman kafin lokacin tashi zuwa shekaranjiya Laraba.
Sai dai da aka zauna shekaranjiya sai shugaban ya bayyana sunayen fitattun mutum 50 daga sassan kasar nan da shugabannin taron za su tuntuba don samun maslaha game da batun kashi biyu bisa uku ko sulusin wakilan taron.
Daga nan ya dage zaman zuwa karfe 4:00 na yamma domin a ba kwamitin damar magance matsalar. Amma da aka dawo dakin taron, sai shugaban ya bada sanarwar dage zaman zuwa ranar Litinin mai zuwa domin ba dattawan 50 damar samar da matsayar da kowa zai amince da ita.
Kwamitin dai ya kunshi Cif Olu Falae da Dokta Kunle Olajide da Janar Ike Nwachukwu da Cif Mike Ahamba, SAN da Cif Peter Odili da Cif Edwin K. Clark da Farfesa Ibrahim Gambari da Farfesa Jubril Aminu da kuma Farfesa Jerry Gana.
Sauran su ne Alhaji Adamu Waziri da Malam Tanko Yakasai da Sanata Ibrahim Idah da Janar A.B. Mamman da A.K. Horsfall da Cif Josephine Anenih da Kwamared Issa Aremu, da Misis Hauwa Ebelyn Shekarau da Hajiya Bola Shagaya da Dokta Olisa Agbakoba, SAN.
Akwai Ambasada bincent Okobi da Ambasada Lawrence Ekpebu da Sanata Femi Okunrounmu da Dokta Joe Nwaogu da Mohammed Umar Kumalia da Farfesa Auwalu Yadudu da Farfesa Iyorchia Ayu da Obong bictor Attah da Sanata Khairat Abdulrazak Gwadabe da Ghali Umar Na’Abba da Sanata Adamu Aliero da kuma Atedo Peterside.
Sai Dokta Chukwuemeka Ezeife da Farfesa Isa B. Mohammed da Kashim Ibrahim Imam da Sanata Florence Ita-Giwa da Sanata Ken Nnamani da Alhaji Bashir dalhatu da Alhaji Sule Yahaya Hamma da Dokta Abubakar Saddikue Mohammed da Cif Olusola Akanmode.
A cikin kwamitin akwai Mai martaba Sarkin Gummi Mai shari’a Lawal Hassan Gummi da Mista Ledum Metee da Mista Fola Adeola da Sanata Mimibariya Amange da Anayo Nebe da Cif Raymond Dokpesi da Benjamin Elue da Janar Alani Akinrenade da Cif Ndukka Obaigbena da kuma Mai shari’a Mamman Nasir.
Tsarin zabe a yayin zaman ne ya raba wakilan inda wakilai daga Arewa suka tsaya kai da fata cewa fasalin ya zamo an samu matsaya ko rinjayen kashi uku bisa hudu kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta sanar.
Sai dai takwarorinsu na Kudu sun nace ne cewa rinjayen kashi biyu bisa uku za a yi amfani da shi, batun da ya jawo takaddamar shiyya a tsakanin wakilan, inda ya jawo zaman taron ya tsaya cik.
Wani wakilin taron ya shaida wa wakilinmu cewa kwamitin ya gaza cimma matsaya ne “saboda dukkan wakilan suna karfafa bukatun da suka dace da su ne, don haka zai yi wahala a samu daidaito,” inji shi.
Wani wakilin kuma ya shaida wa Aminiya cewa, wajibi ne a warware batun fasalin zaben yadda ya kamata. “Za ka iya gani cewa jerin wakilan dama an fifita wani bangare, kuma an yi wa Arewa illa,” inji shi.
“Idan muka amince da jefa kuri’a kan kashi biyu bisa uku kamar yadda mutane Kudu suke bukata, to yana nufin muna nan (wurin taron) a matsayin ’yan kallo ne kawai, saboda mutanen Kudu sun fi mu yawa. Don haka babu amfanin zuwanmu nan, ke nan taron bain da wani amfani,” inji shi.