Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Ya ce majalisar za ta yi aiki da kundin tsarin mulki don tantance duk tanadin ƙudurin tare da yin gyara, a inda ya zama tilas.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Kakakin Majalisar wakilai Tajudeen Abbas

Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce har yanzu majalisar ba ta samar da matsaya kan sabon ƙudirin harajin da Tinubu ya aike musu.

Abbas, ya bayyana hakan ne, yayin jawabinsa kan sabon ƙudirin harajin a zauren majalisar a ranar Litinin.

Sai dai, ya ce majalisar za ta yi aiki da kundin tsarin mulki don tantance duk tanadin ƙudurin tare da yin gyara, a inda ya zama tilas.

Majalisar ta bayyana muhimmancin sauya fasalin tsarin haraji a Najeriya domin samar da tattalin arziƙi mai ɗorewa da rage dogaro da rancen kuɗi.

A gefe guda, majalisar ta jaddada cewa, Najeriya na da ƙarancin haraji idan aka kwatanta da tattalin arziƙinta, inda yawan harajin ya tsaya a kashi 6, yayin da matsakaici haraji a duniya yake a kashi 15.

A cewar majalisar akwai buƙatar a magance hakan domin samar da kuɗaɗen gudanar da ayyuka kamar ilimi, lafiya, da gine-gine.

Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Sauya Fasalin Haraji, Mista Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa, a 2020, kashi 97 na kuɗaɗen shiga na Najeriya ya tafi ne wajen biyan bashi, yayin da hauhawar farashi ya kai kashi 33.

A watan da ya gabata ne fadar shugaban ƙasa, ta aike wa majalisun dokoki ƙudurorin, amma kuma majalisar zartarwa ta bayar da shawarar ƙin amincewa da ƙudurorin saboda wasu sarƙaƙiya da ke tattare da su.

Duk da haka, Tinubu ya ƙi amincewa ya janye ƙudirin.