Ba mu yarda da dokar tilasta shekarun aurar da ’ya’ya mata ba – Sheikh Alhassan Sa’id

A nasa tsokacin kan dokar hana aurar da yara mata har sai sun shekara 18, wani malami mai wa’azin Musulunci Dokta Alhassan Sa’idu Adam Jos, ya ce Musulunci ya halatta duk lokacin da mutum yake so ya aurar da ’yarsa, koda shekararta uku, ko ba ta kai ba, ko da ranar da aka haife ta […]

Ba mu yarda da dokar tilasta shekarun aurar da ’ya’ya mata ba – Sheikh Alhassan Sa’id

Dokta Alhassan Saidu Adam JosA nasa tsokacin kan dokar hana aurar da yara mata har sai sun shekara 18, wani malami mai wa’azin Musulunci Dokta Alhassan Sa’idu Adam Jos, ya ce Musulunci ya halatta duk lokacin da mutum yake so ya aurar da ’yarsa, koda shekararta uku, ko ba ta kai ba, ko da ranar da aka haife ta ne mahaifinta yana da damar ya zaba mata miji. Ya ce manyan malamai sun yi bayanai a kan cewa idan mutun ya ba da ’yarsa tana karama, ko tana shan nono ga wani, abin da za a yi idan wanda aka aurar wa yarinya yana son yarinya ta kai har lokacin da ta samu kanta ta fara hankali, ta samu tarbiyya da ilimi daidai gwargwado, to shi ne za a bar ta har wani lokaci.
Sheikh Alhassan ya ce A’isha ’yar Abubakar, matar Manzon Allah a duniya da Lahira tana da shekara shida ya aure ta da kuma ta kai shekara tara Manzon Allah (SAW) ya kira ta dakinsa, daga ranar ta zama cikakkiyar mace.
Ya ce, shekarun aurar da ’ya mace sun danganta da yadda uba ya ga halin ’yarsa, idan mai tarbiyya ce da  mutunci da kamun kai, uba ya ga zai iya kyale ta ta kai shekara 10 ko 12 ko 18, ko yana so ta yi karatun zamani, ko sana’ar noma, ko kiwo, to, yana da damar ya bar ta, “ Wannan ganin damarsa ce, amma ba a yanke wata doka da ’yarka ba za ta yi aure ba sai ta shekara18, mu a ganinmu Musulunci ake kokarin rusawa. Da an zo mana da maganar kaciyar mata aka ce yana sa yoyon fitsari, mu kuma mun karanta Hadisan Manzon Allah (SAW) cewa kaciyar mata na kara wa mata kyau da sauransu, duk da cewa nan kasar ba ma yi amma wadansu kabilumu na Arewa kamar Shuwa Arab da Yarbawa, suna yi,” inji shi.
Ya ce “Turawa suna kawo irin wadannan abubuwa ne domin su hana addininmu zaman lafiya. A baya sun kawo shawara cewa mutum ba zai tsawatar wa dansa ba, ba za ka doke shi ba, alhali a kasarsu, sai da ya zo ya bugi ubansa, ko ya harbe shi, ko ya tafi tsirara yadda ya ga dama, to abin da suke yi a can shi suke so ya hade duniya, wannan fada ne da Allah.”
Ya ce dama Allah Ya bayyana cewa Yahudu da Nasara ba za su yarda da Musulmi ba har sai ya bi hanyarsu, saboda haka kada ku bi su ba daidai ba ne, “mu ba mu yarda da hukuncinsu ba kuma ba za mu yi musu biyayya ba, muna nan a kan bin dokar Allah. Kuma duk dan majalisa da ya ce sai ya kafa mana wannan doka to mun san ba mu yake wakilta ba, yana wakiltar Turawan Yamma ne, wakilinsu ne, dan rakiyarsu ne, kuma dan kanzaginsu ne, kuma in muna da iko za mu yi masa tawaye, mu ce ya dawo, ko kuma mu tsine masa,” inji shi.
Shi kuma Babban Daraktan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya Farfesa Lawal Khalid ya ce aurar da yarinya, a karacin shekaru ba ya haifar da wani cuta, kamar yadda wani kwararen likita mai suna Mista Tes ya ce kamar yadda aka fake da cewa wai aurar da yarinya da kankanan shekaru yana haifar da matsalar yoyon fitsari ba gaskiya ba ne. Ya ce maimakon a yi dokar hana aurar da mata a karancin shekaru, ya fi dacewa a samar musu da ingantantun asibitoci da za su rika zuwa awo da zarar sun samu juna biyu.

Dokar tana fada da addini ne
– Sheikh Abubakar Jibril

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Dokar haramta aurar da ’ya’ya mata sai sun shekara 18 fada ne da addinin Musulunci, kuma duk wani musulmi dan majalisa da ya rungume hannu ya bari aka fara aiwatar da wannan musiba, yin haka na iya sanya ya halaka.
Sheikh Abubakar Jibril ne ya bayyana haka a Sakkwato a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya game da watsi da wannan kudiri da Majalisar Dattawa ta yi a makon jiya. Ya ce, “Kafin su kawo wannan doka kamata ya yi su fara dokar ciyar da yara mata kyauta, ka ga idan gwamnati ta ciyar maka da ’yarka har ta girma tana da hakkin ta yi yadda take so da ita, ammn an kyale ka da fafutikar kula da ’yarka tun haihuwarta har ta girma lokacin da ya dace ka aurar da ita, sai a ce za a yi dokar da za ta hana ka don kawai rashin adalci,” inji shi.
Sheikh Jibril ya ce duk lokacin da ka zauna ka yi nazari sai ka ga ba kasa wadda ba a san abin da ake yi ba sama da Najeriya a ce kare yana da ’yancinsa kwalbar Mirinda na da ’yancinta amma Bil’adama ba ya da ’yancin, sai yadda ake so za a yi da shi. In ban da shirme mene ne dokar haramta yin aure ga yarinyar da ta balaga, ta je ta rika zina ke nan ko, ita zina ta halatta yin aure da wuri ne bai halatta ba?
Ya ce a nan kasar da wuya ka samu yarinya ’yar shekara 14 da ba ta balaga ba, “to duk wadda ta balaga in ta samu mijin aure ba a aurar da ita ba ana nufin ta yi mi ke nan?”
Sheikh Abukakar Jibril ya ce, “Ba wanda zai hana mu yin addininmu, dokar nan sun kyauta da suka zuba ta a kwandon shara don ba al’umma ake so da alheri ba.”

Dokar tsari ne na Turawa  – Hurumi

Daga Nasiru Bello, Sakkwato

Alhaji Mustafa Bala Hurumi dan majalisa ne mai wakiltar Bodinga ta Kudu a Jihar Sakkwato kuma sananne ne da ya sha gwagwarmayar siyasa, kafin ya zama daya daga cikin masu shata doka a jihar. Aminiya ta tuntube shi kan dokar haramta wa mace aure sai ta kai shekara 18:
Aminiya: Kana ganin dokar haramta aurar da yarinya sai ta kai shekara18 ta dace?
Alhaji Hurumi: A gaskiya a wurina duk wata doka da za ta ci karo da addini na ba na tare da ita. Wannan doka da ake son kakaba mana tsari ne na Turawa da ba ta dace a zo mana da ita ba, don mu wata kasa ce mai ’yanci ba komai aka ga dama sai a zo mana da shi ba, musamman in ya saba al’adarmu da addininmu, wadanda sun yarda da zarar mace za ta iya zaman gidan miji kuma ta samu mijin a aurar da ita, kuma takan cimma wannan matsayar ta kowace irin shekara daga shekara 14, don haka ban goyi bayan wannan dokar ba don ta yi karo da tsarinmu da ka’idojinmu.

Mu duk inda addini yake nan muke – Liman  Malam Safiyanu

Daga John D. Wada, Lafiya

Malam Safiyanu Musa Limamin Babban Masallacin Juma’a na Bukan-Sidi a Lafiya Jihar Nasarawa cewa ya yi  “Addininmu na Musulunci ya koya mana cewa har idan aka ce Allah Ya ce “kaza’’ to, a nan muke. Kuma a gaskiya kamar yadda addininmu ya nuna mana, idan ’ya mace ta kai shekara 12 ubanta bai aurar da ita ba, tofa duk laifi da ta aikata yana kansa ne. Saboda haka idan ’ya mace ta kai shekara 12 mahaifinta ya ki yi mata aure duk laifi da ta diba yana kansa ne. Wato misali a ce tayi zina da wasu laifuffuka a kan ubanta laifin yake. Ana iya ganin wannan umarni a cikin Littafin Attaura. Wannan hakki ne da ya rataya a wuyarsa a matsayinsa na mahaifin yarinyar ya tabbatar ya yi mata aure a wannan lokaci. Saboda haka ban goyi bayan wannan doka na cewa sai ’ya mace ta kai shekara 18 kafin a aurar da ita ba, don ba haka Allah Ya fada ba. Wannan kauce wa ayar Ubangiji ne. Ka ji nawa ra’ayin ke nan na gode.”