Ba mu yarda da tsarin raba shugabancin Majalisun Tarayya ba —Akeredolu

Akeredolu ya bayyana matakin a matsayin wani gadar zaren da ake shirya wa Tinubu.

Ba mu yarda da tsarin raba shugabancin Majalisun Tarayya ba —Akeredolu

Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu

Gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya yi fatali da tsarin raba mukaman shugabancin Majalisun Tarayya wanda jam’iyyar su ta APC da kuma Zababben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu suka amince da shi.

Gwamnan ya bayyana tsarin a matsayin wanda yake tattare da rashin adalci, kana kuma ya saba wa tsarin raba dai-dai da jam’iyyar su ke jagorancin wajen ganin kowanne bangare ya shiga an dama da shi a tafiyar dimokuradiyar kasar.

A makon nan ne jam’iyyar APC ta bayyana goyan baya ga takarar Sanata Godswill Akpabio a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa tare da Sanata Barau Jibrin a matsayin mataimaki.

Haka kuma, jam’iyyar ta bayyana goyon baya ga Tajudeen Abas a matsayin Shugaban Majalisar Wakilai tare da Benjamin Kalu a matsayin mataimaki.

Akeredolu ya ce abin takaici ne yadda shiyyar Arewa maso Yamma ta samu manyan kujeru biyu a majalisa, yayin da wasu yankunan basu da mukami ko da guda.

Gwamnan yace na farko ba a yi tsari mai kyau ba wajen gabatar da wadannan mutane a matsayin shugabanni ba tare da tuntuba da kuma dogon nazari ba.

Kazalika, ya ce an yi watsi da sauran ’yan takarar da ke neman shugabancin ba tare da neman amincewar su ba.

Akeredolu ya kuma bayyana matakin a matsayin wani gadar zaren da ake shirya wa Zababben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu domin ganin shugabancin sa ya samu matsala tun daga matakin farko.

Gwamnan ya kuma koka da yadda takwarorinsa na APC suka kasa taka rawar da ta dace wajen sasanta wannan matsala, domin ganin kowacce shiyya ta samu akalla kujera guda a sabuwar gwamnatin mai zuwa.

Akeredolu ya ce bai ga dalilin da za a baiwa shiyyar Arewa maso Yamma kujeru biyu na shugabancin majalisa ba, yayin da shiyyar Arewa ta Tsakiya za ta tashi a tutar babu.

Yayin da ake wannan, ’yan takara 7 da ke neman shugabancin Majalisar Wakilai yau sun gabatar da korafi ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu domin nuna masa rashin amincewarsu da matakin da jam’iyyar ta dauka dangane da shugabancin majalisar.

Daga cikin wadanda suka halarci ganawar har da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Ahmed Idris Wase da Yusuf Gagdi.