Ba mu yarda da yunkurin kashe Zakzaky ba – Almajiransa

Mabiya Shi’a masu goyon bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky a karkashin kungiyar ’Yunkurin Musulunci sun gudanar da zanga-zangar lumana da jerin gwano a ranar Juma’ar da ta gabata domin la’antar yunkurin da suka yi zargin ana yi na hallaka jagoran nasu. Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun zargi Gwamnatin Tarayya da shirin kashe jagoransu, domin dadada wa […]

Ba mu yarda da yunkurin kashe Zakzaky ba – Almajiransa
Ba mu yarda da yunkurin kashe Zakzaky ba – Almajiransa

Mabiya Shi’a masu goyon bayan Sheikh Ibrahim Zakzaky a karkashin kungiyar ’Yunkurin Musulunci sun gudanar da zanga-zangar lumana da jerin gwano a ranar Juma’ar da ta gabata domin la’antar yunkurin da suka yi zargin ana yi na hallaka jagoran nasu.

Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun zargi Gwamnatin Tarayya da shirin kashe jagoransu, domin dadada wa kasahen Amurka da Isra’ila da suka ce suna nuna kiyayya gare shi, sakamakon jajircewarsa da kasancewa a sahun gaba wajen zarginsu da shirya hare-haren ta’addanci a yankin jihohin Arewa maso Gabas, domin su mallake dimbin dukiyar man fetur da ke jibge a yankin.
Kakakin kungiyar Dokta Abdullahi danladi ya ce almajiran malamin sun gudanar da zanga-zangan lumana a biranen Abuja da Kaduna da Zariya da Sakkwato, domin la’antar wannan shiri, kuma kungiyar ta nanata zargin cewa gwamnatin ce ke daukan nauyin hare-haren da ake dangata su da Boko Haram, kuma ta zargi manyan Arewa da yin shiru a kan al’amarin, saboda gudun abin da ka iya biyo baya, lamarin da ta ce ya sa sun kasance kaskantattu.
Wakilin Zakzaky a Jihar Katsina Malam Yakubu Yahaya ne ya jagorancin zaman dirshan da almajiran malamin suka yi a harabar babban masallacin Juma’a na Katsina don nuna damuwarsu, inda ya ce,”Akwai yunkurin da gwamnatin Jonathan ke yi na hallaka Zakzaky kamar yadda bincikenmu ya nuna, saboda Sheikh Zakzaky ne babbar matsalar Isra’ila da Amurka a kasar nan yanzu.”
Malam Yakubu Yahaya ya ce tsayin Dakar da Sheikh Zakzaky ya yi kan zargin gwamnati da hannu a kashe-kashen da suke faruwa a Arewa maso Gabas ne suka jawo aka kashe ’ya’yansa uku da almajiransa 31, a cikin azumi. Sannan a Potaskum a cikin wannan wata aka kashe masa almajirai sama da 50 mafi yawansu kananan yara da mata.
Ya ce ganin malamin yana nan kan bakansa ne suka ba da wa’adin wata daya na a kashe Zakzaky, “daga gidansa zuwa inda ya koyarwa a Zariya sun ajiye sojoji, kullum sai Malam ya canja hanya… ana ganin wadannan sojoji wadanda wasu Turawa ne a bayan motoci jeep-jeep.”
Almajiran malamin na Gombe ma sun yi jerin gwano inda jagoransu Malam Muhammad Abare Adamu Bajoga, ya nuna rashin amincewarsu kan yunkurin kashe Sheikh Zakzaky.
Malam Muhammad Abare ya bayyana wa manema labarai a Gombe bayan kammala gangamin cewa bayan jama’a da ake ta kashewa sai ga shi an tunkari manyan malaman Musulunci musamman Sheikh Zakzaky da ake neman kashe shi.
Malam Abare Bajoga, ya ce muddin wasu tsiraru za su fito suna kashe jama’a gwamnati ba ta magance ba to suna zargin akwai sa hannunta a ciki domin ita take da hakkin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shugaban ya ce idan gwamnati ta gaza wajen kare jama’a yana da kyau mutane su fito su nuna rashin amincewarsu domin da aka kashe mutane a Yadin Buni da Potiskum da Mubi da sauran wurare ba ’yan Shi’a kawai aka kashe ba, har da ’yan Izala da ’yan darika da Kiristoci.
Shi kuwa jagoran ’yan Shi’a a Jihar Filato Malam Adamu Tsoho kira ya yi ga malaman addinin Musulunci da sarakunan da sauran shugabannin Arewa su fito su yi magana kan kisan gillar da ake yi wa al’umma a yankin Arewa da sunan Boko Haram.
Malam Adamu Tsoho ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabi a wurin gangangamin da ’yan Shi’a suka shirya a Jos don la’antar yunkurin kashe jagoransu Sheikh Zakzaky kamar yadda suka yi zargi.
Ya ce abin bakin ciki ne shugabannin su yi shiru kan miyagun abubuwan da suke faruwa a Arewacin saboda suna tsoron kada a kashe su.
Ya ce an wayi gari a jihohin Barno da Yobe da Adamawa kananan hukumomi da dama suna hanun ’yan Boko Haram, kuma a kullum suna kashe mutane amma an yi shiru. “Haka za mu yi ta zama ana ta kashe mu har sai an gama da mu baki daya?”
Malam Adamu Tsoho ya ce tun lokacin da aka fara wannan wasan kwaikwayo na Boko Haram, Sheikh Zakzaky ya ce gwamnati ce Boko Haram. Ya ce kowa ya san Amurka ta ce nan da shekara ta 2015, Najeriya za ta ruguje. “Don haka suka shirya wannan wasan kwaikwayo na Boko Haram a Arewa,” inji shi.
Ya ce a kullum gwamnatin Jonathan tana kulle-kullen kashe Sheikh Ibrahim Zakzaky, saboda yadda yake tona musu asiri a kan maganar Boko Haram. Ya ce ba za su yarda da wannan mummunan kuduri nasu ba, don haka suka shirya wannan gangami domin nuna rashin amincewarsu.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi