Ba mu yi sama-da-fadi da kudin da aka ba mu ba- AMP, AGN

Shugaban kungiyar furodusoshi ta AMP na kasa Zik Zulu Okafor da Babban Sakataren kungiyar Jaruman Najeriya (AGN), Abubakar Yakubu sun mayar da martani kan takardar kuka da kungiyar Furodusoshi ta ANCOP ta shigar ga Hukumar EFCC da SFU kan cewa  sun yi sama da fadi hade da raba Naira miliyan 50 da Gwamnan Jihar Akwa […]

Ba mu yi sama-da-fadi da kudin da aka ba mu ba- AMP, AGN
Ba mu yi sama-da-fadi da kudin da aka ba mu ba- AMP, AGN

Shugaban kungiyar furodusoshi ta AMP na kasa Zik Zulu Okafor da Babban Sakataren kungiyar Jaruman Najeriya (AGN), Abubakar Yakubu sun mayar da martani kan takardar kuka da kungiyar Furodusoshi ta ANCOP ta shigar ga Hukumar EFCC da SFU kan cewa  sun yi sama da fadi hade da raba Naira miliyan 50 da Gwamnan Jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio ya ba ‘yan fim ba bisa ka’ida ba, ba tare kuma da amincewar wadanda abin ya shafa ba.
A makon da ya gabata ne ANCOP ta rubuta takardar kuka hade da bukatar EFCC ta binciki shugaban kungiyar AMP na kasa, Zik Zulu da Shugaban kungiyar Daraktoci na kasa, Andy Amenechi da Babban Sakataren kungiyar Jaruman Najeriya, Yakubu Abubakar da jaruma Stephanie Okereke- Linus Idahosa kan mummunan rawar da suka taka wajen rabon kudin ba tare da amincewar wadanda abin ya shafa ba.
Sai dai a lokacin da Zik Zulu yake mayar da martani ne ya ce, ANCOP ba ta cikin wadanda abin ya shafa don haka bai ga dalilin da zai rika daga jijiyar wuya ba.
Ya ce: “Mun fara samun matsala da shugaban ANCOP Aled Eyengho a 2009 a lokacin shi ne Babban Sakataren AMP na kasa, a wannan shekarar sai ya nemi mukamin mataimakin shugaban kungiyar bayan ya fadi zabe sai ya kafa ANCOP don zama kishiyarmu. Haka ya rika shiga yana fita don ganin duk wani abu da muka sa a gaba bai yi nasara ba, mun kira shi don a fahimci juna amma ya yi kunnen-uwar-shegu da mu.”
“ANCOP ba ta cikin Nollywood, domin akwai kungiyoyi 10 a karkashin Nollywood da suka hada da MOPPAN da ke Kano da UMPAN da gabashin Najeriya da ANTIP da ke Kudu maso Yamma da sauransu, amma babu ANCOP. Don haka ban ga dalilin da Eyengho zai kalubalance mu ba. Dangane da Naira miliyan 50 da Gwamna Akpabio ya ba mu kuma mun yi abin da ya dace, kuma kungiyoyin da suke karkashinmu sun gani a kasa.” Inji Zik
Babban Sakataren kungiyar Jaruman Najeriya, Yakubu Abubakar ya ce ba su sanya lauje cikin nadi wajen rabon kudin ba don haka ba sa tsoron amsa gayyatar EFCC idan har ta bukaci su je ofishinta.
Ya ce: “Ba mu yi sama-da-fadi da kudin da aka ba mu ba, duk kungiyoyin da abin ya shafa mun yi musu bayanin komai kuma sun gamsu, ANCOP ne suke da wani kulli da ya hana su fahimtar gaskiya. A yanzu batun na gaban ’yan sanda. Na kuma ji dadin hakan domin za su yi bincike kuma ina fata za a hukunta duk wani mai laifi.”