‘Ba mu yi watsi da batun kamfanin jiragen Najeriya ba’
Hukumar da ke Kula da Filayen Jiragen sama ta kasa (FAAN), ta ce gwamnatin tarayya ba ta yi watsi da shirin samar da kamfanin jiragen sama mallakar Najeriya ba.Hukumar ta ce gwamnatin tarayya tana taka tsantsan a kan lamarin wanda tuni kwamitin da aka kafa ya fara tantancewa da kuma bayar da shawarwarin da za […]
Hukumar da ke Kula da Filayen Jiragen sama ta kasa (FAAN), ta ce gwamnatin tarayya ba ta yi watsi da shirin samar da kamfanin jiragen sama mallakar Najeriya ba.
Hukumar ta ce gwamnatin tarayya tana taka tsantsan a kan lamarin wanda tuni kwamitin da aka kafa ya fara tantancewa da kuma bayar da shawarwarin da za su zama alheri ga kasar, kamar yadda BBC ta bayyana.
Wannan dai yana zuwa ne a yayin da ‘yan Najeriya ke korafin cewa gwamnati ta yi watsi ko shiru da lamarin.
Tun bayan da kamfanin jirage na Nigerian Airways mallakin gwamnatin kasar nan ya ruguje dai, ba a kara wani kokari don farfado da shi ba.