Ba mu za a rabawa N70b ba – Ƴan Majalisa
Ƴan majalisar tarayya sun musanta cewa za a raba musu N70 biliyan daga cikin kasafin N819 biliyan da suka sahhalewa shugaban ƙasa. A ranar Alhamis Majalisar Dattawa ta amincewa shugaba Bola Tinubu kashe N500 biliyan kan sassauta raɗaɗin janye tallafin man fetur da kuma N319 biliyan kan wasu ayyukan gwamnatin tarayya. Ayyukan sun haɗa da […]
Ƴan majalisar tarayya sun musanta cewa za a raba musu N70 biliyan daga cikin kasafin N819 biliyan da suka sahhalewa shugaban ƙasa.
A ranar Alhamis Majalisar Dattawa ta amincewa shugaba Bola Tinubu kashe N500 biliyan kan sassauta raɗaɗin janye tallafin man fetur da kuma N319 biliyan kan wasu ayyukan gwamnatin tarayya.
Ayyukan sun haɗa da N185 biliyan na gyaran hanyoyin da ambaliyar ruwa ta lalata, N192 biliyan na gyaran gonakin da ambaliyar ruwa ta lalata, N35 biliyan naira ga hukumar kula da harkokin shari’a ta ƙasa, N10 biliyan ga ayyukan Birnin Tarayya da N70 biliyan ga Majalisar Dokoki ta ƙasa.
Za a kashe wa sababbin ’yan majalisa biliyan 70 a matsayin kudaden ‘maraba’
Majalisa ta sahale wa Tinubu ya kashe N500bn don rage radadin cire tallafin mai
Sai dai shugaban kwamitin yaɗa labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu (APC- Ekiti ta Kudu) ya ce ba ƴan majalisa za a rabawa wannan N70 biliyan ɗin ba.
Sanata Adaramodu ya ce za a yi amfani da kuɗin ne wurin gyara da samar da kayan aiki a ofisoshin ƴan Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa.
A cewarsa “A yanzu haka ƴan majalisa da dama an bar su da saya wa ofisoshinsu kujeru, tebura, da kayan laturoni bayan sauran gyare-gyaren da suka yi.”
Ya kuma ce babu wani ɗan majalisa da za a bai wa kuɗin gyaran a hannunsa, inda ya ce hukumar majalisar ce za ta yi amfani da kuɗin wurin gudanar da gyare-gyaren da samar da kayan aiki kai tsaye.