Ba mu zabi Ahmad Lawan a matsayin dan takarar Shguaban kasa ba —APC

NWC na APC ya ce babu kamshin gaskiya a labarin da ke cewa jam’iyyar ta dauki Ahmad Lawan a matsayin dan takara tilo

Ba mu zabi Ahmad Lawan a matsayin dan takarar Shguaban kasa ba —APC

Hedikwatar Jam’iyyar APC ta Kasa ta karyata labarin da ke yawo cewa ta zabi Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, a matsayin dan takarar shugaban kasar jam’iyyar.

Kwamitin Gudanarwa na Kasa na Jam’iyyar APC na Kasa (NWC) ne ya sanar da haka a yammacin ranar Litinin.

Jam’iyyar ta sanar da hakan ne bayan bullar wani labari da ke cewa ta zabi Ahmad Lawan a matsayin dan takara tilo, a yayin da ake shirin gudanar da zaben dan takarar shugaban jam’iyyar a ranar Talata.

Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sulaiman Argungu ya ce labarin kanzon kurege ne ake yadawa game da daukar Ahmad Lawan.

Ya bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar daga yankin Arewa da kuma Kudu sun yi ittifaki cewa a bai wa dan yankin Kudu takarar, don haka babu yadda za a yi sabanin hakan.

Aminiya ta gano cewa jam’iyyar ta tashi haikan wajen ganin ta fitar da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023 ta hanyar masalaha, babu hamayya.

Daliget 2, 340 ne dai za su kada kuri’ar zaben fitar da dan takarar shugaban kasar a zaben 2023 a ranar Talata.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya