Ba na bukatar zama mataimakin shugaban kasa-Tinubu

Jigo a jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa zai maye gurbin Farfesa Yemi Osibanjo a zaben 2019. Inda ya ce wannan labarin ba komai bane illa zuki-ta-malle. A wani rahoto da Jaridar SUN ta buga, ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo na shirye-shiryen komawa aikinsa na Fasto baki […]

Ba na bukatar zama mataimakin shugaban kasa-Tinubu

Jigo a jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa zai maye gurbin Farfesa Yemi Osibanjo a zaben 2019. Inda ya ce wannan labarin ba komai bane illa zuki-ta-malle.

A wani rahoto da Jaridar SUN ta buga, ta ruwaito cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osibanjo na shirye-shiryen komawa aikinsa na Fasto baki daya, sannan kuma ana tunanin cewa za a maye gurbinsa ne da Tinubu.

A cewar Tinubu “Da ni da mutanen yankin Kudu maso Yamma mun yarda kuma mun amince da wakilci da aiki da Farfesa Yemi Osibanjo ke yi a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa,” inji shi.