Ba na cikin tube Sarki Sunusi II- Buhari
Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce, shugaba Buhari baida hannu wajen tube Sarki Muhammadu Sanusi II daga gadon sarautar Kano. A cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban ya fitar Malam Garba Shehu, ranar Laraba na cewa mai taken “A fitar da Shugaba Buhari daga cikin sha’anin masarautar Kano.“ ya bayyana cewa duka maganganun […]
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Muhammadu Sanusi II
Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce, shugaba Buhari baida hannu wajen tube Sarki Muhammadu Sanusi II daga gadon sarautar Kano.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban ya fitar Malam Garba Shehu, ranar Laraba na cewa mai taken “A fitar da Shugaba Buhari daga cikin sha’anin masarautar Kano.“ ya bayyana cewa duka maganganun da ake yadawa ba gaskiya bane kuma siyasa ce.
Tsohon gwamnan Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Muhammadu Buhari da hannu a cire Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da gwamnan Kano ya yi a ranar Litinin.
Kwankwaso, wanda shi ne mutumin da ya nada Sanusi a shekarar 2014, ya ce abin da ya faru a jihar lamari ne “na bakin ciki, wanda duk gwamnati mai daraja ba za ta aikata ba”.
Sanata Kwankwaso, wanda shi ne jagoran ‘yan adawa a Kano kuma jigo a jam’iyyar PDP ta kasa, ya shaida wa BBC Hausa cewa “shugabannin gwamnati na Kano su da kansu ne ke cewa umarni aka ba su (su tube Sarki Sanusi).
Shi [Buhari ne] ya ba su umarni,” sai dai bai bayar da wasu shaidu da suka tabbatar da hakan ba.
Da umarnin Buhari aka tube Sarki Sanusi II – Kwankwaso