Ba na daka ta mutane – Pete Edochie

Shahararran jarumin fina-finan Kudancin Najeriya (Nollywood) Pete Edochie ya ce ba ya damuwa da yamididin da mutane suke yi a kansa.Pete Odochie mutum ne da ba kawai a Najeriya ake ba shi da kima da daraja ba har a kasashen ketare ana martaba shi, inda hakan ba ya rasa nasaba da yadda yake gudanar da […]

Ba na daka ta mutane – Pete Edochie

Shahararran jarumin fina-finan Kudancin Najeriya (Nollywood) Pete Edochie ya ce ba ya damuwa da yamididin da mutane suke yi a kansa.
Pete Odochie mutum ne da ba kawai a Najeriya ake ba shi da kima da daraja ba har a kasashen ketare ana martaba shi, inda hakan ba ya rasa nasaba da yadda yake gudanar da aikinsa ba tare da kama hannun yaro ba.
 A kwanakin baya an rika yada jitar-jitar cewa ya mutu amma daga bisani ta tabbata yana raye.
dan wasan ya ce bai damu da duk abin da  mutane ke fada game da shi ba.
“Ko kadan ba na damuwa da abin da mutane suke cewa game da ni ba; ina da tsarin da nake tafiyar da rayuwata kuma ya samo asali ne daga irin dabi’un da na ginu akansu.” Inji shi.
Da aka tambaye shi ko akwai wani rol da ba zai iya fitowa a wasan kwaikwayo ba sai  ya ce “ina so na ga na fito a kowane irin rol a wasa, amma matsalar ita ce irin zubi da tsarin da Allah ya yi mini na fi dacewa da basarake, soboda a irin wannan matsayi ne za ka gan ni tamkar Sarki ne na zahiri. Ba wai ina koda kaina ba ne, na san da wadanda nake kama.”
dan wasan ya kara da cewa akwai lokacin da suke daukar wani fim sai aka ba shi rol din talaka, an umarce shi da ya je wani kogi don ya yi fatsa. Bayan ya sanya tufafin da ake zuwa kamun kifi ne, sai nan take mutanen da ke wurin suka fara surutai cewa matsayin bai dace da shi ba.
A ganin Pete Edochie irin surar da Allah Ya yi masa ke hana shi damar fitowa a kowane irin matsayi. “Kodayake ni ma ina jin dadin hakan.” Inji shi.