Ba na gaba da Ali Nuhu- Nura M Inuwa
A kwanakin baya aka rika yada jita-jitar an hana mawaki Nura M Inuwa waka, sannan aka ce ba ya ga maciji da Ali Nuhu. Wakilin Aminiya ya tattauna da mawakin inda ya karyata batun ya daina waka da kuma gaskiyar magana dangane da dangantakarsa da Ali Nuhu. Ga yadda hirar ta kasance:Ina gaskiyar jita-jitar da […]
A kwanakin baya aka rika yada jita-jitar an hana mawaki Nura M Inuwa waka, sannan aka ce ba ya ga maciji da Ali Nuhu. Wakilin Aminiya ya tattauna da mawakin inda ya karyata batun ya daina waka da kuma gaskiyar magana dangane da dangantakarsa da Ali Nuhu. Ga yadda hirar ta kasance:
Ina gaskiyar jita-jitar da ake yadawa cewa an hana ka waka?
Ba gaskiya ba ne cewa na daina waka. Ba a kuma hana ni ba, amma na san komai daren dadewa zan daina, saboda ko ba mutuwa akwai tsufa. Don haka ina so mutane su fahimta, komai lokaci ne, idan zan daina waka, to zan daina ta ne a lokacin da ya kamata ba sai na tsufa ba. Zan daina waka ne saboda in bar wa ’yan baya, don su samu damar ba da gudunmuwarsu a harkar, duk da cewa na san damar a wurin Allah take, kuma Shi ke ba wanda Ya so, a lokacin da Ya so.
A yanzu dai ban kai lokacin da zan daina waka ba, amma don Allah masu yada jita-jita a kaina su daina, domin komai na Allah ne.
An ce ba ka ga maciji da Ali Nuhu, dalilin da ya sa ba ya ba ka wakoki idan kamfaninsa zai shirya fim ke nan, me ya hada ku?
To ni dai a iya sanina ban san wata matsala da ta shiga tsakanina da Ali Nuhu ba, don haka babu komai tsakani na da shi.
Me ya ja hankalinka har ka fara daukar nauyin shirya fina-finai baya ga waka?
Waka dai sana’ata ce, don haka na fi ba ta karfi a kan komai, shi kuma fim a bangare guda wani abu ne da zai tallafa min cikin harkokina, shi ya sa nake daukat nauyin shirya fim.
Da gaske ne kana cikin ’yan fim din da za su je Indiya kwas?
A’a, ni ban san da tafiyar ba ma sai yanzu da ake tambaya ta. Amma ina yi musu fatan alheri, ina son duk wani abu da zai kara daukaka masana’antarmu.
Wacce matsala ke ci ma ka tuwo a kwarya a harkar shirya fim da kuma waka?
To matsalar dai ba ta wuce hassada ba, duk matsalar da Kannywood ta samu kanta a ciki, to faru ne dalilin hassada. Kuma al’amura ba za su daidaita ba sai an daina hassada.
Yaya kake hada waka da kuma daukar nauyin shirya fim?
To, wannan abu ne mai sauki, zan iya cewa ni ba furodusa ba ne, sai dai mai daukar nauyi a kamfaninmu na Abnur Entertainment, domin muna da furodusa, wato Abdul Amart ke nan, to ka ga ba ni da wata damuwa a kan hakan.
Wacce shawara za ka ba masu kallo?
To masu kallonmu su dinga ba mu shawara tagari, sannan kada su dinga yawan aibata mu a kan abin da ba su da tabbas a kai. Ina so su daina yarda da jita-jita.