Ba na goyon bayan amfani da Naira biliyan 37 don gyaran majalisa- Dan Majalisa
Daya daga cikin dan Majalisar dokokin tarayya, Bamidele Salam, ya yi watsi da ta shirin kashe kudaden da suka kai har Naira biliyan 37 don gyaran ginin majalisar tarayyar, wanda Dan Majalisar ya bayyana yin hakan a matsayin kuskure. Hon. Bamidele, mai wakiltar mazabun Ede ta Arewa/Ede ta Kudu/Egbedore/Ejigbo a jihar Osun. Ya bayyana hakan […]
Tushen dimokuradiyya: Majalisar Dokokin ta Kasa
Daya daga cikin dan Majalisar dokokin tarayya, Bamidele Salam, ya yi watsi da ta shirin kashe kudaden da suka kai har Naira biliyan 37 don gyaran ginin majalisar tarayyar, wanda Dan Majalisar ya bayyana yin hakan a matsayin kuskure.
Hon. Bamidele, mai wakiltar mazabun Ede ta Arewa/Ede ta Kudu/Egbedore/Ejigbo a jihar Osun. Ya bayyana hakan ne sakonsa na a shafin tiwita, in da ya bukaci Majalisar ta yi amfanin da kudaden wajen bayar da rance ga masu kananan sana’o’I a kasar.
Dan manjalisar, ya kara da cewa “Ba na tunanin Majalisar na bukatar wadannan kudaden wajen yin gyara. Dakunan karatu, asibitoci da hanyoyi sun fi muhimmanci a gyara a yanzu.”