Ba na kyamar Musulmi – Shugaba Jonathan
Shugaban Goodluck Jonathan ya ce ba ya amfani da ofishinsa wajen nuna kin jinin Musulmi kamar yadda wadansu ke zarginsa da aikatawa.Mai magana da yawun shugaban kasa Reuben Abati ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa ’yan jarida jawabi a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin.Shugaban kasar ya mayar […]
Shugaban Goodluck Jonathan ya ce ba ya amfani da ofishinsa wajen nuna kin jinin Musulmi kamar yadda wadansu ke zarginsa da aikatawa.
Mai magana da yawun shugaban kasa Reuben Abati ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa ’yan jarida jawabi a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Litinin.
Shugaban kasar ya mayar da martani ne sakamakon zarginsa da kungiyar kare hakkin Musulmi mai suna MURIC ta yi cewa, yana amfani da mukaminsa wajen yada akidun Yahudawa.
Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishak Akintola a cikin wata sanarwa da ya fitar a makon jiya, ya zargi Jonathan da yin amfani da karfin ofishinsa wajen sanya wani tambari mai yada akidar Yahudawa a sabuwar Naira 100 da ya kaddamar a makon jiya.
Abati ya ce zargi ne marar tushe da kuma makama, inda ya jaddada Jonathan shugaba ne na kowa ba tare yana nuna bambancin addini ba.
Ya ce “An jawo hankalinmu cewa kungiyar da ke kare hakkin Musulmi ta fitar da sanarwa mai dauke da sa hannun daraktanta Farfesa Ishak Akintola, inda suka zargi Shugaba Jonathan da nuna kin jinin Musulmi. Ina so Akintola ya fahimci Jonathan ba ya kin jinin Musulmi. Jonathan shugaban kasa na kowa ne, ba ya nuna bambancin kowane addini.”
Ya ce, babu gaskiya ko miskala zarratan cewa shugaban kasa yana yada akidar Yahudawa.
“Shugaban kasa ba ya yada akidar Yahudawa, abin takaici ne a ce wannan sanarwar ta fita daga wurin Akintola na kungiyar MURIC, ya kamata su nemi afuwa a wurin Shugaba Jonathan.
“MURIC ta ce tambarin da yake jikin Naira 100 ana kiransa ‘Star of Dabid, wanda tambarin Yahudawa ne, ina so a fahimta wannan tambarin bai yi kama da tambarin ‘Star of Dabid’, ko wane abu da yake nuna alaka da akidar Yahudawa ba. Tambarin ‘Star of Dabid’ yana dauke da zane mai kusurwa uku (triangle) guda biyu da aka hada su, idan an duba sabuwar Naira 100 za a ga tambarin bai yi kama da ‘Star of Dabid’ ba. Don haka wannan tambari ne da yake samar da tsaro ga sabuwar Naira 100.
“Wannan tambarin zai ba jama’a damar tantance Naira 100 mai kyawu da kuma da ta jabu. Wannan tambari an hada kusurwa hudu (skuares) guda biyu ne, sannan aka hada launin ma’adanin Manila brikuette, wanda aka yi amfani da shi a matsayin kudi a lokacin Turawan mulkin mallaka.” Inji Abati.
Abati ya kuma ga baiken kungiyar inda ta ce an danne ko tauye Musulmi a lokacin da aka gudanar da taron kasa, inda ya ce hakan abin takaici ne.
“An gudanar da taron kasa bisa kamala, batun addini bai taka wata rawa yayin taron ba. Dandalin taron ya zama wata kafa da aka tattauna batutuwan da suka shafi komai na kasa ne.”
Abati ya kuma karyata batun da kungiyar MURIC ta yi cewa jami’an tsaro daga kasar Isra’ila ne suke ba fadar shugaban kasa tsaro.
A karshe ya bukaci MURIC ta daina karkatar da hankalin jama’a a kan al’amuran kasa, don cimma biyan bukatarta.