Ba na kyamar ’yan Arewa – Jonathan

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa ta kashe kudi yawa domin kawar da cutar shan-inna a yankin Arewa. Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da jirgin kamfe dinsa ya isa Sakkwato, inda ya ce, ba domin rikicin da ake fama da shi a yankin Arewa maso Gabas ba, da yana iya bayyana babu […]

Ba na kyamar ’yan Arewa – Jonathan
Ba na kyamar ’yan Arewa – Jonathan

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya ce gwamnatinsa ta kashe kudi yawa domin kawar da cutar shan-inna a yankin Arewa. Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da jirgin kamfe dinsa ya isa Sakkwato, inda ya ce, ba domin rikicin da ake fama da shi a yankin Arewa maso Gabas ba, da yana iya bayyana babu sauran cutar shan-inna a kasar nan.

Shugaba Jonathan yana mayar da martani ne kan abin da ya bayyana da karairayin da ake gaya wa mutanen Arewa game da shi domin a bata masa suna. “Akwai karairayin da ake gaya wa mutanen Arewa. Kada ku zabi Jonathan, Jonathan ba ya son Arewa. Amma an sha tambaya, lokacin da na hau mulki na gina jami’o’i 14, kuma hudu daga cikin jami’o’in nan 14 suna Kudu ne 10 kuma suna Arewa. Idan ba na son Arewa, ko ban son yaran Arewa su kasance kamata, ba na jin zan gina jami’o’i 10 a yankin,” inji Jonathan.
Ya ce idan yana kin Arewa ba zai kashe kudi masu yawa kan makarantun allo ba. Ya ce fiye da kashi 70 cikin 100 na kasafin aikin gona an kashe su ne a Arewa, inda ya kalubalanci tsofaffin shugabanni musamman wadanda suka fito daga su fadi jami’o’i ko makarantu nawa suka gina wa yankin.
Kuma ya kalubalance su shaida wa mutanen Arewa ta wace hanya suka taimaka wajen bunkasa yankin a bangaren aikin gona da harkokin sufuri.
Jonathan ya ce, mafi yawan matsalar cutar shan-inna da ya gada a Arewa take. Shugaban ya kuma yi fatali da zargin nuna son kai wajen rabon ayyukan da Gwamnatin Tarayya take gudanarwa.
Game da zargin cewa yana ingiza wutar ayyukan ta’adda ne domin a kasa gudanar da zabe, ya ce babu wani tanadi a tsarin mulki da ya ce wani Shugaban kasa zai iya zama a kan kujerar mulki fiye da shekara hudu.
Lokacin da tawagar Shugaban kasar ta kai ziyarar ban girma ga Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya bukaci Shugaban kasar ya yi kokari wajen shawo kan tashin hankalin da ke aukuwa a Arewa maso Gabas, tare da kira ga ’yan siyasa da kada idonsu ya rufe wajen furta kalaman da za su iya jawo matsala maimakon gina kasa. “Mu zauna da junanmu ta hanyar girmama addinin kowa ta haka ne zai sanya a girmama naka addinin,” inji shi. Ya ce har yanzu shi kansa bai samu katin jefa kuri’arsa na dindindin ba, kamar yadda miliyoyin jama’a ba su karba ba.