Ba na nadamar barin PDP -Labaran Maku

A ’yan kwanakin nan ne wadansu jiga-jigan jam’iyyar PDP ciki har da shugaba Goodluck Jonathan suka zargi tsohon ministan yada labarai Labaran Maku kuma dan takarar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar APGA da cewa ya bijire wa jam’iyyarsu. wakilinmu ya tattauna da Labaran Maku a Lafiya don jin ta bakinsa game da zargin, inda […]

Ba na nadamar barin PDP -Labaran Maku

A ’yan kwanakin nan ne wadansu jiga-jigan jam’iyyar PDP ciki har da shugaba Goodluck Jonathan suka zargi tsohon ministan yada labarai Labaran Maku kuma dan takarar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar APGA da cewa ya bijire wa jam’iyyarsu. wakilinmu ya tattauna da Labaran Maku a Lafiya don jin ta bakinsa game da zargin, inda ya mayar da martani. Ga dai yadda hirar ya kasance: 

Aminiya: Me za ka ce game da zargin da wadansu jiga-jigan tsohuwar jam’iyyarka PDP ciki har da shugaban kasa Goodluck Jonathan ke yi cewa Jonathan bai umurce ka ka canja sheka zuwa jam’iyyar APGA ba?
To ai ni tun farko ma abin da nakes o jama’a su fahimta shi ne ban taba bayyana cewa Jonathan ya umurce ni in canja sheka daga jam’iyyar PDP zuwa ta APGA ba. Don ina da cikakken sanin cewa bai kamata a ce shugaban kasa da ke kujera ya goyi bayan wani dan takara daga wata jam’iyya daban ba. Saboda haka na riga na sani cewa abu ne da ba zai yiwu ba, kuma ina da sanin haka tun farko. To me zai sa in nemi goyon bayansa a yakin neman kujerar gwamnan jihar nan da nake yi? Abin da ke ba ni mamaki shi ne yadda wadansu jiga-jigan jam’iyyar PDP, kamar su shugaban majalisar dattawa Dabid Mark da Amadu Ali da Adamu Mua’zu da sauransu, ke ta zagina don ina yi wa Jonathan kamfen don tabbatar da ya samu nasara, musamman a nan jihata Nasarawa. Ina so su sani cewa, ina yin haka ne ba don komai ba sai don na tabbata Jonathan ne kawai zai iya gudanar da kyakkyawan mulki a kasar nan idan aka sake zabensa, kamar yadda yake yi a yanzu. Don kamar yadda ka sani na yi aiki da shi a matsayin minista na tsawon lokaci na san wane irin shugaba ne shi. Shugaba ne adali mai rikon amana. Kuma ina so in nanata cewa kowa ya sani cewa sabuwar jam’iyyata, wato APGA, ta bayyana wa al’ummar kasar nan baki daya cewa ba ta da dan takarar shugaban kasa a inuwarta, saboda haka za ta mara wa Janathan baya a zaben badi, wato Jonathan tamkar dan takarar shugaban kasa a inuwarta ne. To idan haka ne, kuma don na fito a matsayina na dan APGA yau ina yi masa kamfen a nan jihar Nasarawa na yi laifi ke nan? Kuma maimakon shi Dabid Mark ya yi kokarin cire abin da ke idonsa sai yana ta zargina babu gaira babu dalili. Ya ce ba ni da godiya na bijire wa PDP bayan na ci moriyarta, ya kuma ce zan cigaba da faduwa har karshen rayuwata da sauransu. Ka ga ba magana ce da yakamata a ce shugaba kamarsa da nake girmamawa sosai ya yi ba. Kuma ai akwai wadansu jiga-jigan PDP daga jiharsa Binuwai, kamar su tsohon ministan kasuwanci da zuba jari (Trade and Inbestment) Dokta Sam Ortom da tsohon shugaban PDP na kasa Sanata Barnabas Gemade da sauransu, da bayan sun canja sheka sun kuma fito takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar adawa wato APC. Har yanzu da muke magana Dabid Mark bai ce komai game da su ba. Saboda haka ina shawartarsa da ya je ya dawo da wadannan mutane PDP ya daina sa baki cikin batun canja shekana don na yi ne da kyakkyawar manufa, wato kawo karshen mulkin kisa da ake yi a jihar nan.
Kuma kowa ya sani cewa an tafka mini magudi sosai a zaben fidda gwani da jam’iyyar PDP ta yi kwanakin baya inda aka baiwa Alhaji Yusuf Agabi a maimakona. Saboda haka ina so in yi amfani da wannan damar in sake nanata cewa rashin adalci da son kai ne da ke jam’iyyar PDP, musamman a jihar nan suka sa na canja sheka zuwa APGA.
Aminiya: Kafin ka canja sheka zuwa APGA wane mataki ka dauka bayan sakamakon zaebn fidda gwanin na PDP da aka bayyana Yusuf Agabi a matsayin wanda ya yi nasara?
Babu shakka na bi hanyoyin da suka dace wajen ganin an yi gyara a wannan zabe dake cike da kurakurai. Na kai kara gaban wani kwamiti da jam’iyyar ta kafa don sauraran koke-koken sakamakon zaben fidda gwani na PDP a kasar nan baki daya, wanda shi kansa shugaban jam’iyyar na kasa Alhaji Adamu Mua’zu ke shugabanta. Na bayyana irin kurakurai da magudi da aka tafka a zaben da a karshe aka bayyana Alhaji Yusuf Agabi a matsayin wanda ya yi nasara. Amma abun mamaki da bakin ciki shi ne, wannan kwamitin bai ma gayyaci shi Yusuf Agabi ya kare kansa daga zargin ba, balle ya dauki wani mataki a kan batun, maimakon haka sai ya yi watsi da karar baki daya. Akwai adalci a nan? Saboda haka kamar yadda na bayyana ne a baya, akwai abubuwa da dama da suka sanya ni barin PDP zuwa APGA da idan zan bayyana duka za mu dauki tsawon lokaci ban kare ba. Ka ga na kasance daya daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar PDP a jihar nan na kuma bauta mata sosai. Amma sai aka wayi gari yau aka ce ba a son ire-irenmu a jam’iyyar, babu gaira babu dalili. Saboda haka ya kasance mini dole ne in canja sheka. Na yi kuma ba na da na sani.
Aminiya: Yaya gaskiyar maganar da wadansu ke yi cewa don ba a son Kirista ya shugabanci jihar nan ne ya sa aka bai wa Agabi tutar takarar gwamna na PDP?
Haka yake gaskiyar lamarin ke nan, wasunmu da dadewa mun lura cewa akwai wadansu shedanu a jihar nan da dama daga dukkan alamu ba sa son Kirista ya shugabanci wannan jihar. Ba maganar ra’ayi ba ne, gaskiyar magana ce. Babu shakka kamar yadda nake bayyanawa kullum, zan sake bayyanawa cewa wannan makirci da sharri da nake fuskanta yanzu duk saboda ni Kirista ne, kuma ina da sha’awar shugabancin jihar nan. Saboda haka ni dai ban dauka wannan batu da muhimmanci ba, don na tabbata galibin al’ummar jihar nan da suka san abin da suke yi sun sani cewa da musulmi da kirista daya muke. Akwai wadansu ‘yan uwana da suke musulunci kuma muna zauna lafiya. Wadansu shedanu kalilan ne kawai suke so su maida komai na addini. Wadannan mutane suna ta kashe-kashe a jihar nan ba don komai ba don a sa mutane kamata su hakura da neman kujerar mulkin jihar nan. Amma ina so in tabbatar musu cewa zan cigaba, ba zan karaya ba har sai na kwato ragamar mulkin jihar nan, in kawo karshen mummunan shugabanci. Don mun zauna lafiya da juna a jihar nan na tsawon lokaci babu wata matsala. To me ya sa ake ta kasha kashen nan yanzu? Al’ummar jihar nan daya ne da musulmi da kirista, amma sai yau wani ya zo zai raba mu, ba za mu yarda ba sai mun canja shi. Don idan Allah Ya ce yau kirista zai shugabanci jihar nan babu mahalukin da zai iya hanawa, haka ma idan Ya ce musulmi ne zai shugabance ta babu wanda ya isa ya hana.
Aminiya: A karshe wane sako kake da shi ga al’ummar jihar nan baki daya?
Ni dai kiran da zan yi ga al’ummar jihar nan baki daya, musamman magoya bayan sabuwar jam’iyyata APGA shi ne, kada su kula da wannan makirci da barazana da wadansu jiga-jigan PDP ke yi mini, don na tabbata suna yi ne saboda dan takaransu a nan jiha Yusuf Agabi ya yi nasara. Su fito kwansu da kwarkwata kamar yadda suka yi alkawari su kada wa APGA kuri’unsu a zabe mai zuwa don ceto su daga wannan bala’i na fadace-fadace da suka samu kansu yau. Su kuma zauna lafiya da junansu. Ni kuma ina nan a APGA daram ba gudu ba ja da baya.