Ba na nadamar yi wa Buhari fatan mutuwa – Gwamnan Ekiti

Gwamnan Jihar Ekiti, Peter Ayodele Fayose ya ce ba ya nadama game da tallar da ya dauki nauyin bugawa a wasu jaridu na ranar Litinin da ta gabata, inda ya bayyana cewa akwai yiwuwar Janar Buhari ya mutu. Ya ce ba zai yi nadama ba, saboda bayanin da ya yi yana da ‘kanshin gaskiya.’ Gwamna […]

Ba na nadamar yi wa Buhari fatan mutuwa – Gwamnan Ekiti

Gwamnan Jihar Ekiti, Peter Ayodele Fayose ya ce ba ya nadama game da tallar da ya dauki nauyin bugawa a wasu jaridu na ranar Litinin da ta gabata, inda ya bayyana cewa akwai yiwuwar Janar Buhari ya mutu. Ya ce ba zai yi nadama ba, saboda bayanin da ya yi yana da ‘kanshin gaskiya.’

Gwamna Fayoshe dai a ranar Litinin da ta gabata ce, a wata tallar jarida da ya dauki nauyin bugawa, ya yi hasashen cewa akwai yiwuwar idan aka zabi dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya mutu a kan mulki kamar yadda wasu shugabannin kasa uku daga Arewa su ma suka mutu. Shugabannin kasa uku da gwamnan ke magana a kai sun hada da marigaya Umaru Musa ’Yar-aduwa da Janar Sani Abacha da kuma Janar Murtala Mohammed.
A yayin da al’umma daban-daban a fadin kasar nan suka yi Allah-wadai da wannan talla, a matsayin abin da bai dace ba, shi kuwa Fayose, a wata sanarwa da ya fitar a Ado Ekiti a Talatar da ta gabata, wacce ke dauke da sa hannun Babban Sakatarensa na Watsa Labarai, Mista Idowu Adelusi ya ce ba za a ci gaba da boye gaskiya har abada ba. Kamar yadda ya ce, dan takarar shugabancin kasa a tutar APC, Janar Muhammadu Buhari (ritaya) ‘ya tsufa kuma ba ya da lafiya’ don haka ba zai iya shugabancin kasa ba.
Gwamnan ya ce wannan talla da ya dauki nauyin bugawa, ra’ayin kansa ne a matsayinsa na dan kasa, ba ra’ayin jam’iyyar PDP ba, sannnan kuma ya kara da cewa “ba na nadama.”
“Zan so in kafa misali da marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar-aduwa, wanda tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce yana da isassar lafiyar jagorancin kasar nan, amma daga bisani ya shiga rashin lafiya kuma ya mutu daga baya.
“Ya zama dole in tabbatar wa wadanda suka nuna damuwa, ba kamar APC ba da suke wasa, suna sanya siyasa kan batun ba, ni ba niyyata ce in nufi Janar Buhari da mutuwa ba amma nufina shi ne in bayyana ainahin gaskiyar da APC ke boyewa.”
“Dalilin da ya sa na zabi in tallata batun rashin lafiyar marigayi Shugaban kasa, shi ne saboda in tuna wa kasar nan irin matsalar da ta jefa mu a 2010, har sai da Majalisar Tarayya ta ceto mu, bayan kungiyar Ceto Najeriya (SNG) ta nuna bukatar haka.
“Domin a tabbatar da adalci ne ya sanya muka yi kira don mu kauce wa faruwar matsala, idan aka ce Janar ya ci zabe kuma ya mutu, sai mataimakinsa, wanda ya fito daga Kudu maso yamma ya ce zai dare mulki.
“Ina jan hankalin mutane game da labarin da jaridar Sunday Tribune, ta ranar 18 ga Janairu, 2015, mai taken ‘Niyyar Buhari na tafiya Amurka ta tada kura.’
“Labarin ya bayyana cewa an kammala shirin kai Buhari Amurka domin binciken lafiyarsa. An ce Buhari ya gaji a sakamakon tafiye-tafiyen yakin neman zaben shugabancin kasa, don haka yana matukar bukatar a duba lafiyarsa. Haka kuma an ce tsufa ya cin masa, wanda haka ke kara haddasa masa matsala.”
Fayose ya shawarci Buhari da ya yi wa kansa adalci, ya aje takarar shugabancin kasa da yake yi, ya bar matashi mai jini a jika da karsashi. “Na kara fadin cewa Buhari ya tsufa kwarai, ba zai iya mulkin Najeriya ba.” Inji shi.
Sai dai kuma Kwamitin Yakin Neman Zaben Goodluck Jonathan ya nisanta kansa da batun Fayose. Ya ce wannan talla da Fayose ya yi, ba ra’ayin Shugaba Jonathan ko ta kwamitin kamfen dinsa ba ce.