Ba na neman matsayin Shugaban Masu Rinjaye – Wamakko

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltaar mazabar Sakkwato ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko ya karyata labaran da wasu jaridu suka buga, na cewar ya na neman mukamin shugaban masu rinjaye a majalisar ta dattawa. Ya ce shi ba ya neman kowanne irin mukami a cikin majalisar,  a cewarsa, “Bani da sha’awar neman mukamin shugaban majalisa, ko […]

Ba na neman matsayin Shugaban Masu Rinjaye – Wamakko

Dan Majalisar Dattawa mai wakiltaar mazabar Sakkwato ta Arewa, Aliyu Magatakarda Wamakko ya karyata labaran da wasu jaridu suka buga, na cewar ya na neman mukamin shugaban masu rinjaye a majalisar ta dattawa.

Ya ce shi ba ya neman kowanne irin mukami a cikin majalisar,  a cewarsa, “Bani da sha’awar neman mukamin shugaban majalisa, ko makamancin hakan, kuma ni ban shiga takarar nema ba,’’ a sanarwar da mataimakin na mussaman akan harkokin yada labarai ga Sanata Wamakko, Bashir Rabe Mani tana cewa duk labarin da jaridu suka buga na cewar yana neman mukamin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan karo na 9 ba bu gaskiya a cikinsa.

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa

Masu zanga-zanga sun tare babbar hanyar Abuja kan matsalar tsaro

Janar Rabe Abubakar ya rasu a hannun ’yan bindiga