Ba na nuna wariyar launin fata – Shugaba Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi ba mai nuna wariyar launin fata ba ne bayan an zarge shi da siffanta kasashen Afirka a matsayin kasashen kasakantattu. Rahotanni sun ce shugaban ya yi amfani da kalmar ne na kaskanci a makon jiya yayin da yake wani taro kan batun shige da fice a fadarsa kamar […]

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi ba mai nuna wariyar launin fata ba ne bayan an zarge shi da siffanta kasashen Afirka a matsayin kasashen kasakantattu.
Rahotanni sun ce shugaban ya yi amfani da kalmar ne na kaskanci a makon jiya yayin da yake wani taro kan batun shige da fice a fadarsa kamar yadda BBC ta ruwaito.
Wannan furucin na Trump ya janyo cece-kuce a tsakanin kasashen na Afirka, da wasu bangarorin duniya, ciki har da Majalisar dinkin Duniya.
Da Trump ya ji matsin lambar ya yi yawa, shi ne ya bayyana wa manema labarai cewa: “Ni ba mai nuna wariya ba ne. Ni ne mutumin da na fi duk wani mutum da kuka taba ganawa da shi karancin nuna wariyar launin fata.”