Ba na son zama uban gidan kowa a siyasar Kaduna — El-Rufai
Alaƙa dai ta fara tsami tsakanin tsagin El-Rufai da Uba Sani a Jihar Kaduna.
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewar ba ya son ya zama uban gidan kowa a siyasa a jihar.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron bita da aka shirya wa ma’aikatan gwamnati a Jihar Borno.
- Zargin Rashawa: APC ta dakatar da Ganduje
- Ya Kashe ’Yan Mata 3 ’Yan Gida 1 A Yawon Sallah A Nasarawa
El-Rufa’i, ya bayyana burinsa na ganin gwamnan Jihar Kaduna mai ci, ya yi shugabanci mai nagarta, ba tare da ya tsoma masa baki ba.
El-Rufa’i ya jaddada muhimmancin shugabanci tare da hadimai masu hazaƙa, domin a cewarsa babu wanda zai iya yin komai shi kaɗai.
Wannan dai na zuwa ne, biyo bayan takun-saka tsakanin El-Rufai da magajinsa Sanata Uba Sani a jihar.
Idan za a tuna, yayin wani taro a jihar, gwamna mai ci, Uba Sani ya bayyana ɗimbin bashin da El-Rufa’i, ya bar wa jihar.
Gwamnan, ya koka kan yadda kuɗaɗen jihar ke zurarewa ta hanyar biyan bashin da gwamnatin baya da bar wa jihar.
Sai dai a wancan lokaci, ɗan tsohon gwamnan, Bello El-Rufai, ya soki gwamna mai ci, inda ya ce gwamnan ya zagaye kansa da mutanen da ba su iya komai a barci.
A cewarsa hakan ya sanya gwamna Sani gaza taɓuka komai, shi ya sa ya fake da cewar mahaifinsa ya lafta wa jihar ɗimbin bashi.
Hakan ya sanya alaƙa ta fara tsami tsakanin ɓangarorin biyu; na tsohon gwamnan da kuma gwamna mai ci.
Amma alaƙar ta ƙara tsami ne yayin da jami’an DSS suka cafke Aisha Galadima, wadda ta hannun damar El-Rufai ce, kan zargin yada kalaman cin zarafi a kan gwamna Sani a shafukan sada zumunta.
Wasu majiyoyi sun ce Galadima, ta soki gwamnan jihar na yanzu ne kan kalaman da ya yi a kan uban gidansa.
Sai dai mai magana da yawun gwamnan, Muhammad Lawal Shehu, ya bayyana cewar ba shi da masaniya game da kamen da DSS suka yi mata.