Ba na tsoron mutuwa amma ina son na yi sulhu da gwamnati — Bello Turji 

Sai an daina kashe mana ’yan uwanmu sannan za mu daina kashe mutanen Zamfara.

Ba na tsoron mutuwa amma ina son na yi sulhu da gwamnati — Bello Turji 

Bello Turji

Ɗaya daga cikin ƙasurguman ’yan bindigar da ake nema ruwa a jallo, Bello Turji, ya yi wa jami’an tsaro tutiyar cewa ba ya tsoron mutuwa.

Sai dai a yayin da yake wannan iƙirarin, Bello Turji ya ce yana kiran gwamnati zuwa teburin sulhu domin kawo ƙarshen ta’addanci a Jihar Zamfara.

Turji yana ɗaya daga cikin fitattun ’yan bindiga 43 a Arewa maso Yammacin Nijeriya da Rundunar Sojin Nijeriya ta ayyana nema ruwa a jallo.

Cikin wani saƙon bidiyo mai tsawon minti biyar da daƙiƙa 40 da ya fitar, Bello Turji ya ce kisan ubangidansa, Halilu Sububu da sojoji suka yi a bayan nan ba zai razana shi ba.

Bello Turji ya ce a shirye yake ya ajiye makamai muddin gwamnati za ta amince da tayin zama a teburin sulhu tare da shi.

A cewar Turji, “kamar yadda ’yan baƙin ciki ke cewa sauri ƙiris a share mu daga doron ƙasa, to mu dama ba mu zo wannan duniya ba don a share mana wurin mun zauna.

“Mu dama a kodayaushe jira muke yi a kashe mu. Saboda haka muke tabbatar wa mutane, tun daga zamanin sahabbai ake kashe mutane da Annabawa duk ana ta kashewa.

“Saboda haka muke tabbatar wa mutane da al’ummar Jihar Zamfara baki ɗaya, ba ma tsoron a kashe mu.

“Ba ma tsoron a jefo mana bam ko a yi mana wani abu.

“Amma al’ummar Zamfara muna faɗa muku kalma ɗaya wadda har yanzu ba ku fahimta ba. Idan kuka bar kashe mana ’yan uwanmu za mu daina kashe ku.

“Gwamna Dauda Lawal da Bello Matawalle ba za su taimake ku ba. Ina so al’ummar Zamfara su gane cewa su [Lawal da Matawalle] ‘yan siyasa ne ba ta ku suke ba, babu muradin al’ummar Zamfara a cikin zukatansu.

“Lokacin da Matawalle yake gwamna wane ne yake ɗaukar nauyin mu? Lokacin da Abdulaziz Yari yake gwamna wane ne yake ɗaukar nauyin mu? Babu wanda ke ɗaukar nauyin mu da taimakon mu sai Allah.

“A zamanin mulkin Yerima ne gwamnati ta sayar da filayen kiwo sannan ta halasta kashe Fulani.

“Lokacin da Mahmud Shinkafi ya hau mulki, ya yi ƙoƙarin magance matsalar amma bai yi nasara ba. Da Abdulaziz Yari ya zo sai ya ƙara wa ’yan banga karfi da har yanzu muna fama da su.

“Don haka ne muke kira ga dukkan ku da ku zo ku ba mu haɗin kai domin a samu zaman lafiya a yi mulki a daina zubar da jini a Zamfara.

“Bindigogi da kawo hare-hare ta sama ba za su hana mu ba don ba ma tsoron mutuwa.

‘Kashe Halilu Sububu ba zai firgita mu ba’

“Kachallah Halilu Sububu ba shi ne mutum na farko da aka kashe ba; an kashe wasu da dama.

“Kisan Halilu Sububu ba zai hana mu yin abin da muke yi ba, har sai kun daina kashe ’yan uwanmu a jihohin Zamfara, Sakkwato, Katsina, da Neja.

“Shirin ku kawai shi ne ku kawar da kabilar Fulani alhalin Allah ya kare mu. Ko ka kashe mu, Allah ne ya kaddara haka, amma ba da ikonka ba.”

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba