Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku

Fadar shugaban ƙasa ta ce Atiku na yi wa Tinubu hassada ne saboda ya kada shi a zaɓen 2023.

Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku

Tinubu da Atiku

Fadar Shugaban Ƙasa, ta ce Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, yana baƙin ciki da matsayin Shugaba Bola Tinubu na Shugaban ƙasa.

Fadar ta ce muƙamin da ɗan takarar jam’iyyar PDP a 2023, ya nema bai samu, wanda ya yi ta nema har sau shida, amma bai yi nasara ba.

Fadar ta soki Atikun ne saboda shawarar da ya bayar a kan sauye-sauyen tattalin arziƙi da matakan yaƙi da cin hanci da rashawa.

Sai dai, Atiku ya ce, ba ya yi wa Tinubu hassada, inda ya ce ya jefa ’yan Nijeriya cikin ƙunci.

Ɗan takarar Shugaban ƙasar ƙarƙashin Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, ya mayar da martani kan ta yi cewa, yana ƙyashi tare da baƙin ciki da matsayin Shugaba Bola Tinubu na Shugaban ƙasa.

Wata sanarwa da mai bai wa Shugaban ƙasar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ta soki Atiku tare da magoya bayansa kan yadda suke sukar shugaba Tinubu.

A baya-bayan nan dai, Atiku ya buɗe wuta musamman a kafafen watsa labarai, inda yake sukar tsare-tsaren da Tinubu ke bijirowa.

A cewar tsohon mataimakin shugaban ƙasar, ya ce wasu daga sauye-sauyen da Tinubu ya kawo musamman ta fuskar tattalin arziƙi, sun jefa miliyoyin jama’a cikin ƙangin talauci maimakon samar musu da sauƙi.

Turmutsutsun abinci: Najeriya na fuskantar annobar yunwa – LP

An yanke wa direba hukuncin kisa kan kashe mutum 35 a China

Lalacewar jirgin ƙasa ya sa fasinjoji sun maƙale a Delta

Jerin Manyan Dambarwan Kano a 2024