Ba ni aka kama a Saudiyya ba – Sanata Barata
A ranar Lahadin da ta wuce ne tsohon Sanatan Adamawa ta Kudu, Sanata Hassan Barata ya musanta labarin da ake yadawa cewa an kama shi kuma yana tsare a hannun ’yan sandan kasar Saudiyya.Sanata Barata ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne domin bai je Saudiyya ba yana nan a Najeriya.Da yake jawabi ga […]
A ranar Lahadin da ta wuce ne tsohon Sanatan Adamawa ta Kudu, Sanata Hassan Barata ya musanta labarin da ake yadawa cewa an kama shi kuma yana tsare a hannun ’yan sandan kasar Saudiyya.
Sanata Barata ya ce wannan labari ba gaskiya ba ne domin bai je Saudiyya ba yana nan a Najeriya.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan ya rako Gwamnan Jihar Adamawa zuwa taron gwamnonin Arewa da aka yi a Kaduna, Sanata Barata ya dora laifin wannan kage da aka yi masa a kan makiyansa da ke bakin cikin farin jininsa na karuwa a cikin jama’arsa.
Sanata Barata ya ce wadansu da ke bakin ciki da ci gaba da ya samu a siyasa musamman a jiharsa ta Adamawa ke neman bata masa suna. “Idan aka ce mutum ya mutu kuma sai ga shi da kansa ya kawo sakon mutuwarsa akwai magana. Ni dai da safe na tashi sai na ji an ce wai an kama ni a Saudiyya. Wai ina hannun ’yan sanda a can kasar ta Saudiyya. Ni kuwa ga shi yanzu ina Kaduna daga Yola na taso mun zo tare da Gwamnan jiharmu, inda kuwa ina Saudiyya ne ai babu yadda zan yi magana da ku a nan,” inji shi.
Ya ce shi dan siyasa a kullun zargi yake yi domin kuwa tafiya yake yana zargi saboda haka yana ganin akwai wadanda ba su jin dadin farin jininsa a siyasance.
Sai ya bukaci da manema labarai su rika tantance labaransu kafin su buga domin kauce wa bata wa mutanen kirki suna