Ba ni ba siyasa – Jarumin Indiya, Salman Khan

A farkon makon nan ne dan fim din Indiya da ke tashe a yanzu, Salman Khan ya barranta kansa da shiga siyasa. Inda ya bayyana wa manema labarai cewa shi ba zai taba shiga harkokin siyasa ba.dan fim din, wanda ya tsoma kansa wajen hidima ga al’umma ta hanyar kungiyoyin  daban-daban a birnin Mumbai da […]

Ba ni ba siyasa – Jarumin Indiya, Salman Khan

Salman Khan a cikin daya daga fina-finansa da ya fito a matsayin jami’in ‘yan sandaA farkon makon nan ne dan fim din Indiya da ke tashe a yanzu, Salman Khan ya barranta kansa da shiga siyasa. Inda ya bayyana wa manema labarai cewa shi ba zai taba shiga harkokin siyasa ba.
dan fim din, wanda ya tsoma kansa wajen hidima ga al’umma ta hanyar kungiyoyin  daban-daban a birnin Mumbai da kewaye, yace maimakon ya shiga siyasa, ya gwammace ya ci gaba da yi wa al’ummarsa hidima ta hanyar kungiyoyin gama kai.
“Ba na sha’awar shiga harkokin siyasa amma dai tabbas zan ci gaba da yi wa al’ummata hidima ta hanyar shiga kungiyoyin gama kai. Ni siyasata ta tsaya ne kawai ga yin aikin ci gaban al’ummata.” Inji Salman Khan a yayin da yake karin bayani ga manema labarai.