Ba ni da alaƙa da masu son raba Kwankwaso da Abba — Bichi

Sakataren gwamnatin ya musanta zarge-zargen da ake masa.

Ba ni da alaƙa da masu son raba Kwankwaso da Abba — Bichi

Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Abdullahi Baffa Bichi, ya nesanta kansa daga ƙungiyar da ake zargin tana ƙoƙarin raba Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Tun da fari an alaƙanta ƙungiyar da sakataren gwamnatin, amma ya musanta duk wani zargi da ake masa.

Yayin da yake magana da manema labarai bayan wata ganawa da gwamnan, ya ce, “Wannan ƙungiyar da ake cewa ina da alaƙa da ita, ban san komai game da ita ba, kuma ba ni da hannu a ciki.”

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da ake zargin Kwankwaso da yin uwa da makarɓiya a cikin wasu muhimman al’amuran gwamnatin jihar, wanda hakan ya sa wasu ke zargin Gwamna Abba Kabir Yusuf ba shi da cikakken iko gudanar da ayyukansa.

Wasu ma na ganin kamar Kwankwaso na yin “zango na uku na mulki a bayan fage.”

Wannan ya sa wasu suka fara shiga gidajen rediyo da sauran kafafen sada zumunta, inda suka shiga kiran Gwamna “Abba Tsaya da Ƙafarka.”

Wani daga cikin ƙungiyar “Abba Tsaya da Ƙafarka”, Kwamared Nura Gambo Rimingata, ya zargi Kwankwaso da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasa.

Ya ce, “Ba za mu sha wahala wajen kafa gwamnati ba, mu bar wani mutum da ake kira jagora ya karɓe ikon gwamna.”

Rimingata ya kuma zargi Kwankwaso da shiryawa tsaf domin tunkarar zaɓen gwamna na 2027, tare da fitar da waɗanda za su zama gwamna, mataimakin gwamna da sakataren gwamnati a Kano.

Duk da haka, wani na hannun damar gwamnan, Alhaji Nagoda, ya ƙaryata waɗannan zarge-zargen, inda ya ce babu abin da ƙungiyar ke shirin yi face yunƙurin tayar da husuma a tafiyar Kwankwasiyya.

Ya gargaɗi waɗanda suke yunƙurin wargaza tafiyar da su guji cin amanar jagoran tafiyar, inda ya kawo misali da irin matsalolin da suka fuskanta bayan sun juya wa shugabanninsu baya.

Nagoda ya ce, “Da ƙafafun wa gwamnan ya tsaya tsawon wannan lokaci?”

Masanin siyasa Farfesa Kamilu Sani Fagge daga Jami’ar Bayero ta Kano, ya yi tsokaci kan wannan rikici.

Ya bayyana cewa irin wannan rikici na samuwa ne saboda rashin martaba dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyu da rashin kyakkyawan tsari na aƙida.

Ya ce, “Jam’iyyun siyasa ba su da tsari na aƙida, sun zama taron mutane daban-daban masu ra’ayoyi daban-daban suna haɗuwa domin kafa gwamnati,” in ji shi.

Wannan rikici ya nuna irin matsalolin da ake fuskanta a siyasar Kano, musamman tsakanin Gwamna Abba da Kwankwaso, wanda wasu suke ganin jagorancinsa yana hana gwamnan ’yancin gudanar da aikinsa.

A gefe guda, wasu na ganin kiran samun ’yanci a matsayin yunƙurin wargaza tafiyar Kwankwasiyya.