Ba ni da asara idan ban zama Gwamnan Katsina ba –Tata
daya daga cikin masu son tsayawa takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben badi, Alhaji Umar Abdullahi Tsauri wanda aka fi sani da Tata, ya ce babu wata asara da zai yi idan har bai samu nasarar zama Gwamnan ba duk da makudan kudin da yake kashewa wajen taimakon jama’a. Alhaji Umar […]
daya daga cikin masu son tsayawa takarar Gwamnan Jihar Katsina a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben badi, Alhaji Umar Abdullahi Tsauri wanda aka fi sani da Tata, ya ce babu wata asara da zai yi idan har bai samu nasarar zama Gwamnan ba duk da makudan kudin da yake kashewa wajen taimakon jama’a.
Alhaji Umar Tata ya bayyana hakan ne a cikin shirin Hannu da Yawa na gidan Rediyon Tarayya na Kaduna a ranar Lahadin da ta gabata.
dan siyasar ya ce jama’a ne suka bukaci ya nemi kujerar Gwamnan Katsina. “Ban taba sha’awar na yi Gwamna ba. Kuma ba ya cikin abubuwan da da nake sha’awa kafin jama’a su bukaci hakan. Ganin irin ayyukan da na gudanar ne sai mutane suka fara cewa “Allah Ya yi ma Gwamnan Katsina a 2015,” inji shi.
Ya ce yana gudanar da ayyukan taimakon jama’a ne ba tare da neman wata biyan bukatar kansa ba.
Game da cewa wasu manyan ’yan siyasa ne suka turo shi don neman biyan bukatarsu, ya ce: “Jama’a kan ce Shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya turo ni Katsina. Sau daya na taba ido hudu da shi. Sai nake cewa a dauka shi ya turo ni. Tun watan Disamban shekarar 2010 muke ayyukan taimakon jama’a. Idan tun lokacin shi ya turo ni, na taimaki wa? Na taimake shi ko na taimaki Gwamna Shema? Da kuma aka gama, don me bai kira ni, ya ce na dawo gida ba, sai ya ce na zauna, na ci gaba? Shema dai ba kara zama Gwamna zai yi ba. Kuma sai ka yi la’akari jiha nawa gare mu a Najeriya. 36, Katsinan nan guda daya ce. Yanzu idan ba a jefa kuri’a a Katsina ba, tana hana a ci zabe? Ka ga don me za a turo ni Katsina ke nan? Wadanda ke son bata ni ke cewa Goodluck ne ya aiko ni, saboda sun ga ayyukan da muke yi kudi ne ke yin su.”
Ya ce, “Akwai wadanda ke cewa aljannu ne ke ba ni kudi, akwai masu cewa ma kungiyar CAN ce ta aiko ni. Idan muka tsaya kan Goodluck ke ba ni kudi yau shekara uku da rabi. In taho Katsina na yi masallaci da hanya da gadoji da makabarta da tura yara makaranta da taimakon marayu da sauran ayyuka birjik. Wannan mutum don Allah idan shi ne yake ba ni kudin, masoyin Katsina ne ko makiyi? Kuma ka taba jin irin Tata da Goodluck ya aika Sakkwato ko Kano? To ka ga idan har Katsina kadai Goodluck zai yi wa wannan abu, Bakatsine yana da hujjar da zai ce Goodluck ba mutumin kirki ba ne?
Game da abubuwan da zai mayar da hankali idan ya zama Gwamna, ya ce: “Duk wani mataki na rayuwa har da aure da zaman aure mun riga mun tsara yadda za a yi shi a jihar littattafan na nan. Ranar Asabar (gobe) zan kaddamar da takarata a cikin birnin Katsina, kuma za mu raba wadannan littattafan ga jama’a. Babban burina shi ne idan na zama Gwamna a cikin wata 20, na samar da wutar lantarki awa 24 a baki dayan jihar.”