Ba ni da dan takara a zaben kananan hukumomin Taraba – Mukaddashin Gwamna
A kwanakin baya ne kungiyar ’Yan jarida ta Najeriya (NUJ), Shiyyar Arewa maso Gabas ta gudanar da taronta na shiyya da kaddamar da wasu kwamitoci a Jihar Taraba a karkashin jagorancin Mataimakiyar Shugaban kungiyar a shiyyar Hajiya A’isha Ibrahim, tawagar ’yan jaridar ta ziyarci Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar inda wakilinmu ya samu yin […]
A kwanakin baya ne kungiyar ’Yan jarida ta Najeriya (NUJ), Shiyyar Arewa maso Gabas ta gudanar da taronta na shiyya da kaddamar da wasu kwamitoci a Jihar Taraba a karkashin jagorancin Mataimakiyar Shugaban kungiyar a shiyyar Hajiya A’isha Ibrahim, tawagar ’yan jaridar ta ziyarci Mukaddashin Gwamnan Jihar Alhaji Garba Umar inda wakilinmu ya samu yin takaitacciyar hira da shi:
Aminiya: Wane yunkuri gwamnatin Jihar Taraba take yi wajen inganta tattalin arziki da rayuwar jama’ar jihar ta hanyar aririta albarkatun da Allah Ya hore wa wannan jiha?
Mukaddashin Gwamna: Alhamdu lillahi mun gode wa Allah, tare da farin ciki da zuwanku wannan jiha tamu. Kun ziyarci yankin Mambila kun ga albarkatun da Allah Ya hore wa wannan jiha, ina shaida wa duniya Gwamnatin Tarayya tana kokarin agaza wa wannan yanki. Saboda a watan jiya a taron da muka yi da Mataimakin Shugaban kasa an tabbatar mana cewa Shugaban kasa ya amince za a gina madatsar ruwa da za ta samar da wutar lantarki da zai wadaci Shiyyar Arewa maso Gabas har a ba wasu yankunan Najeriya. Haka kuma za a gina babban otel a Gembu wato Mambila tare da filin jirgin sama wanda idan baki suka zo za su rika sauka don bunkasa yawon shakatawa.
Ni kuma a matakin jiha na nemi a ba ni izini na gina wannan hanya don al’amrra su gudana a cikin sauki, kuma tuni mun bayar da kwangilar hanyar, da zarar mun samu izni daga Gwamnatin Tarayya, saboda farawarmu shi zai sa a gudanar da komai a cikin lokaci kuma insha Allah duk wasu shirye-shirye sun kankama kan wannan aiki.
Aminiya: Matsalar tsaro da harkokin matasa suke damu duk wata gwamnati a Arewa, me gwamnatinka ke yi kan wannan?
Mukaddashin Gwamna: Game da matasa muna kokari, don a wannan lokaci mun ware matasa sama da dubu takwas mun sanya su a cikin wani shiri na dogaro da kai ta hanyar koya musu sana’a don su lura da kansu. Idan sun gama kuma za mu raba musu kayan aiki don su ci gaba da yin sana’ar da suka koya har su ma su rika koya wa wasu. Saboda matsalar zaman matasa kara-zube ita ce babban abin da ya dame mu, amma mun gode wa Allah saboda matasan wannan yanki suna kokarin neman abin kansu. Don haka muke rokon kowane mutum a wannan jiha ya taimaka mana wajen gyara tarbiyyar ’ya’yansa da na kusa da shi saboda su ne manyan gobe, idan sun lalace, dole al’umma ta samu matsala. Game da tsaro kuma gaskiya mu wannan yanki mun gode Allah, ba mu da wata matsala mai tayar da hankali saboda mun hada kai da jami’an tsaro da mutanen jihar ana zaune lafiya ba wata fitina inda aka samu matsala shi ma an shawo kan lamarin, insha Allah ba abin da zai sake faruwa, don haka muke jan hankalin mutane kowa ya kasance mai kaunar zaman lafiya, don shi ne gaba da komai.
Aminiya: Wane kira za ka yi wa jama’arka game da shirin tunkarar zabubbuka masu zuwa don su gudana cikin nasara?
Mukaddashin Gwamna: Gaskiya ina jan hankalin jama’a kowa ya rungumi juna a zauna lafiya, saboda dukkanmu ’yan uwan juna ne saboda kusan kashi tamanin na mutanen wannan jiha ’yan uwa ne. Kuma Kirista ne da Musulmi da ake yamutse ba gidan da babu mabiya wani addini, ina gani bai kamata mu samu matsala ba, tunda Allah Ya yi mu wuri daya dole mu zauna da juna tare. Game da siyasa mai zuwa ina rokon mu yi siyasa mai nagarta ta yadda wani ba zai yi kuka da wani ba. Kuma wannan gwamnati ba ta da ra’ayi kan goyon bayan wani dan takara ko zaben kananan hukumomi da za a yi nan da wata biyu ba ni da wani dan takara. Kowa ya fita ya zabi wanda yake so, kowa ya zabi wanda zai masa aiki shi ne nake so, kuma duk wanda ya samu nasara mutane suka ce shi suke so mu ma shi muke so. Saboda duk wanda Allah Ya ce zai yi mulki sai ya yi. Don haka ni ma yanzu Allah Ya kawo ni ina yi, ban ga dalilin da idan mutane suka zabi mutum za a murde a hana shi nasarar da ya samu ba.