Ba ni da dangantaka da marigayi S. Nuhu – Sardaunan Mawaka

Abdul’aziz dahiru wanda aka fi sani da Sardaunan Mawaka fitaccen mawaki ne, a hirarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya fara waka, ya kuma tabo jita-jitar da ake yadawa cewa akwai dangantaka tsakaninsa da marigayi Ahmed S. Nuhu: Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?Sunana Abdul’aziz dahiru, mai lakabin Mai Abokan Juna ko Sardaunan Mawakan Hausa […]

Ba ni da dangantaka da marigayi S. Nuhu – Sardaunan Mawaka
Ba ni da dangantaka da marigayi S. Nuhu – Sardaunan Mawaka

Abdul’aziz dahiru wanda aka fi sani da Sardaunan Mawaka fitaccen mawaki ne, a hirarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya fara waka, ya kuma tabo jita-jitar da ake yadawa cewa akwai dangantaka tsakaninsa da marigayi Ahmed S. Nuhu:

Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?
Sunana Abdul’aziz dahiru, mai lakabin Mai Abokan Juna ko Sardaunan Mawakan Hausa ko Garkuwan Matasan Arewa. An haife ni a 1986 a Unguwar Farin Yaro a garin Katsina. Na yi karatun addini, sannan na yi na boko daga firamare har zuwa diploma a kan kwamfuta.
Me ya ja hankalinka ka fara waka kuma yaya aka yi ka samu lakabin sunayen da ka ambata?
Tun da na taso ni mutum ne mai son fadakarwa da zimmar yin wani abu da al’umma za ta amfana, sai na ga zan cimma wannan burin ta hanyar wakoki. Dalilin da na samu lakabin ‘Mai Abokan Juna’shi ne wani littafin Hausa da na taba rubutawa a shekarar 2000 ne, saboda rubuta littattafan Hausa na fara kafin waka. Garkuwan Matasa kuma uwar matasa ta Arewa Hajiya Zulai ta nada mini. Sunan Sardaunan Mawaka kuma sarauta ce da kowa ke kirana da ita tun farkon fara wakata zuwa yau. Sannan sunan da na mayar wa kamfanina shi ne ‘Mai Abokan Juna Entertainment’ kuma da sunan duk albam dina yake fita.
Yaushe ka fara waka, kuma wacce ce Bakandamiyarka ko ta fi ba ka wahala?
Na daina kirga wakokina daga shekarar 2011, amma a lokacin na san ina da wakoki akalla za su kai 3000. Gaskiya Bakandamiyata wacce take babba daga ita ce ‘Mai Girman Daraja’, ita waka ce ta yabon Annabi Muhammadu (SAW).
Wakar da ta fi ba ni wahala ita ce ta wani auren da aka yi na ’yar Mahe Rashid, Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN). Dalilin da ya sa na wahala shi ne, sau uku ina yi tana gogewa kafin a karshe na samu na cire ta.
A komai na rayuwa dan Adam ba za ka raba shi da fuskantar matsaloli ba, a harkar waka wadanne matsaloli kake fuskanta?
Mahassada. Abin da ya sa na ce mahassada, ka san duk wanda Allah Ya daukaka sai ya ga masoya, sai kuma ya ga makiya, amma dai alhamdulillahi.
A kasar Hausa ana yi wa mawaka wani irin kallo, ba ka fuskanci wata matsala daga iyaye ko ’yan uwa da abokai ba?
Eh to, ka san wakokin iri-iri ne, duk wanda ya san wakokina ya san masu tsabta nake yi, ba na yin na batsa, ko wasu da za su sa a kyamace ni, ko a rika zagina.
Wadanne abubuwa za ka lissafa a matsayin nasarorin da ka samu a waka?
To alhamdulillahi, babbar nasara dai ita ce masoya, domin nasarar samun masoya ta fi komai a duniya, sannan ta bangaren kyaututtuka nan ma na samu babu adadi, an yi mini wadanda na ji dadinsu da wadanda suka sanya ni alfahari da waka a rayuwa.
Wane buri kake da shi a harkar?
Ai ni burina har ya cika, domin burina zama da mutane lafiya, na zauna da masoya da abokan sana’ata lafiya, domin a harkar waka ina daga cikin mawakan da duniya ke alfahari da su, kasancewar ba a taba raba ni fada da wani ba kaf industuri. Kuma masoya daga ko’ina a fadin Najeriya da kasashen ketare suna farin ciki da wakokina, suna jin dadi. A koyaushe cikin amsa kira nake safe da yamma kai har ma cikin dare duk daga masoya.
A bangaren abokan sana’arka, su wa ka fi jin dadin aiki da su?
To gaskiya ni duk wanda muke aiki tare ina jin dadi, saboda ni mutum ne da kowa nawa ne, mutum ne mai barkwanci da wasa da dariya, zai yi wuyar gaske mu zauna da kai sau daya ka ga ba ka shaku da ni ba.
Mawaka suna yayin albam walau marar hoto ko na bidiyo, shin ka yi wani shiri a kan haka din?
kwarai kuwa yanzu haka akwai albam dina na yabon fiyayyen halitta (SAW) da nake shiryawa. Biyu daga cikin wakokin a Dubai na yi su, an yi musu kidan Larabawa, sauran wakokin kuma a nan gida Najeriya.
Mene ne jigon wakokinka?
Ilimantarwa da fadakarwa da nishadantarwa da girmama yabo, sai soyayya, ma’ana ina wakokin yabon Rasulillahi, Ina yin na aure da suna da siyasa da sarauta da wakokin girmamawa na manyan mutane.
Na fim fa?
Ban cika yin na fim ba.
Kamar wadanne wakokin fim ka yi?
Kamar fim din labarina mai suna ‘Abokan Juna’ da wasu da ake shirin fara daukarsu.
Ana yada cewa kana da dangantaka da marigayi Ahmad S. Nuhu?
Tabbas ana fadin haka, domin na sha zuwa wurare da kyar nake sha, ko kuma ka ga ana ta kallona, wasu da yawa har yanzu ba su yarda cewa ba ni da alaka ta jini da shi ba, da yawa cewa suke dan gidanmu ne. Kai na ga abu kan maganar kamata da marigayi S. Nuhu, domin akwai lokacin da na je ATM cire kudi kwanaki, wata ta rika kallona har dai ta kasa hakuri, ta ce mini don Allah Malam kai dan gidansu Ahmed S. Nuhu? Sai na yi dariya na ce mata, a’a, abin da ya ja doguwar magana ke nan ta ki yarda muka rabu a haka. Wasu kuma sukan kira ni da Adamu Nagudu, sun ce muna kama.