Ba ni da hannu a dawowar Aminu Ado Bayero Kano — Ribadu

Ribadu ya musanta zargin da ake na cewar yana da hannu wajen haddasa rikici a jihar.

Ba ni da hannu a dawowar Aminu Ado Bayero Kano — Ribadu

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce ba shi da hannu a zargin da ake masa na taimaka wa tsohon Sarkin Kano, Aminu Bayero wajen komawa jihar.

Da sanyin safiyar ranar Asabar ne, Aminu Ado ya koma Kano, inda ya sauka a ƙaramar fadar masarautar jihar da ke Nassarawa, yayin da Muhammadu Sanusi II ya shiga fadar masarautar da ke Gidan Rumfa.

Sai dai lamarin ya haifar da ruɗani a Kano.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin kama Aminu Ado Bayero bayan isarsa jihar.

Mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya yi zargin cewa Ribadu ne, ya taimaka wa Aminu wajen dawowa jihar ta hanyar ba shi jirgin sama da dakarun soji.

“Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro ne ya ba da jirgin sama guda biyu domin kawo Sarkin Kano da aka tsige. Ba mu fahimci manufarsa ba,” in ji Gwarzo.

Sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Zakari Mijinyawa ya fitar, ya ce Ribadu ya bayyana zargin a matsayin “babu gaskiya a ciki”.

“Na karanta maganganun da aka wallafa a kafafen sada zumunta, ba gaskiya ba ne. Hukumar NSA ba ta ba wa kowa jirgin sama zuwa Kano ba.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ya kamata ‘yan siyasa su guji yaɗa maganganu marasa tushe yayin da jami’an tsaro a jihar ke ƙoƙarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.”

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya