Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida

Shekara 41 bayan kisan gogaggen ɗan jarida kuma Babban Editan Jaridar Newawatch Dele Giwa ta hanyar wasikar bom, tsohon Shugaban Ƙasa na mulkin soja Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya nesanta kansa da lamarin

Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida

Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta nesanta hannunsa da kisan gogaggen ɗan jarida kuma Babban Editan Jaridar Newawatch, Dele Giwa.

An kashe Dele Giwa wanda fitaccen mai sukar gwamnatin Babangida ne, ta hanyar wasikar bom a gidansa da ke Legas a ranar 19 ga watan Oktoban 1986.

Kwana biyu kafin kisan nasa wani babban jami’in Rundunar Leƙen Asiri ta Soji ya zargi Dele Giwa da yin fasa-kwaurin makamai da ƙasashen da nufin tayar da zaune tsaye a Najeriya

Sakamakon haka, dan jaridar ya yi hanzarin sanar da lauyansa, Gani Fawehinmi, game da halin da ake ciki.

Amma bayan kwanan biyu, wani babban hafsan soji, Kamar Halilu Akilu, ya kira waya ta ba Dele Giwa tabbacin cewa kuskure aka samu kuma an gano ainihin lamarin, don haka ya kwantar da hankalinsa, komai ya wuce.

Wani abokin Dele Giwa a Newawatch mai suna  Ray Ekpu, ya ce bayan ’yan sa’o’i ne aka kai wani sako gwamnati gidan Dele Giwa.

Ray Ekpu ya bayyana cewa ɗan Dele Giwa mai suna Billy ne ya karbi sakon mai ɗauke da tambarin Fadar Shugaban Ƙasar ya mika wa mahaifin nasa, wanda a lokacin yake cin abinci tare da wakilin Newawatch na London, Kayode Soyinka,  wand ya kawo mishi ziyara.

Wasikar mai ɗauke da tambarin Fadar Shugaban Ƙasa na kuma dauke da rubutun “wanda aka aika wa kaɗai zai buɗe.”

Amma a yanzu shekara 41 bayan kisan na Dele, Janar Babangida ya nesanta hannunsa ko masaniyar lamarin.

Babangida ya nesanta kansa da lamarin ne a littafin Tarihi da da ya ƙaddamar a ranar Alhamis a Abuja.

Babangida ya bayyana fatan cewa wata rana gaskiya ta yi halintama gano hakikanin musabbabin mutuwar Dele Giwa.

Ya bayyana takaici cewa ’yan jarida sun kawo koma baya  ga binciken kisan, inda suka yi saurin yanke hukunci kafin a kammala binciken.

A cewarsa, ya yi fatan a lokacin da gwamantin farar hula ta Olusegun Obasanjo ta sake buɗe binciken kisan Dele Giwa ’yan sanda za su samo sabbin hujjoji da ke nuna abin da ya faru, amma hakan bai samu ba.