Ba ni da hannu a rikicin APC a Jihar Kaduna – El-Rufa’i

Tsohon Ministan Birnin Tarayya, Abuja, kuma Mataimakin Babban Sakataren Jam’iyyar APC ta kasa, Malam Nasir El-Rufa’i ya musanta zargin da ake yi masa cewa yana da hannu wajen haddasa rikicin da ke faruwa a jam’iyyar a Jihar Kaduna. Rikicin da ke faruwa a Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna na kara ruruwa inda har zuwa yanzu […]

Ba ni da hannu a rikicin APC a Jihar Kaduna – El-Rufa’i
Ba ni da hannu a rikicin APC a Jihar Kaduna – El-Rufa’i

Tsohon Ministan Birnin Tarayya, Abuja, kuma Mataimakin Babban Sakataren Jam’iyyar APC ta kasa, Malam Nasir El-Rufa’i ya musanta zargin da ake yi masa cewa yana da hannu wajen haddasa rikicin da ke faruwa a jam’iyyar a Jihar Kaduna.
Rikicin da ke faruwa a Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna na kara ruruwa inda har zuwa yanzu jam’iyyar ta kasa shirya zaben shugabanninta a jihar.
“Duk wanda ya ce ina da hannu a rikicin APC a Jihar Kaduna bai san abin da yake yi ba, domin ni yadda da irin tarbiyar da aka ba ni da karatun da na yi da al’adarmu idan aka ba ka mulki ka yi adalci ka kuma tabbatar an bi dokar da aka saka. Akwai dokokin da aka gindaya amma wasu mutane ’yan kama-karya wadanda ba su ci zabe ba ke neman karya wadannan dokokin. Ni kuma hakkina ne in tabbatar an bi wadannan dokokin,” inji shi.
Ya ce “Saboda na ce a bi doka sai aka ga Abdullahi ne zai ci zabe sai a ce ai ina tare da shi. Gobe kuma idan na ce a bi wancan tsari sai aka lura Muhammadu ne zai ci zabe sai a ce wai ina goyon bayansa. Saboda haka shugaba juji ne dole kowa ya ce ni ke da laifi na kuma karbi laifin,”inji shi.
Malam El-Rufa’i ya kuma bukaci duk wanda ke da korafi a kan zaben shugabanci da aka shirya a jihar da ya kai kara wajen kwamitin sauraron korafi domin samun maslaha a maimakon kawo rikici a jam’iyyar.
“Tsarin mulkin jam’iyyar ya haramta bayyana rikicin jam’iyya ga manema labarai har sai bayan ta kasa yin tsulhu. Amma saboda wasu ba sa son a bi ka’ida suna son sai sun yi mulki dole ko jama’a na son su ko a’a shi ya sa suke korafi,” inji shi.
A game da rikicin jam’iyyar a Jihar Kaduna, sai ya ce “Babu rikita-rikita a APC a Jihar Kaduna maso kawo rigamar sun yi zabe ne aka kayar da su kuma ba su yarda cewa ba su da mutane ba, kuma sun ki kai kara ga kwamitin sauraren korofi domin sun san ko sun kai kara ba su da hujja.”  
Malam El-Rufa’i na mayar da martani ne kan zargin da kungiyar masu takarar shugabancin jam’iyar a Jihar Kaduna a karkashin jagorancin Dokta Hakeem Baba Ahmed suka yi cewa shi da mukarrabansa na da hannu a rikicin da ya mamaye APC a Jihar Kaduna.
Sun bukaci uwar jam’iyyar ta kasa ta rusa wasu daga cikin zabubbukan shugabannin APC a kananan hukumomi da aka yi a ranar Asabar da ta wuce saboda zargin an tafka magudi a lokacin zabubbukan.